Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 15Article 449650

BBC Hausa of Monday, 15 March 2021

Source: BBC

Solskjaer zai cigaba da zama a United, Pogba zai tafi PSG

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer

Manchester United ta shirya taya mai tsaron ragar Burnley Nick Pope, duk da Tottenham itama tana neman golan mai shekaru 28. (Star on Sunday)

Wata majiya kuma na cewa United za ta tsawaita ƙwantiragin mai horar da ƙungiyar Ole Gunnar Solskjaer, yayin da ake hasashen Edinson Cavani da Anthony Martial da kuma David De Gea za su bar ƙungiyar. (Sunday Mirror)

Mai horar da Juventus ya ce jita-jita ce kawai ake yadawa cewa Cristiano Ronaldo zai bar ƙungiyar. (Football Italia)

Paris St-German ta tuntuɓi wakilin dan wasan Manchester United Paul Pogba don duba yiwuwar sayen ɗan wasan tsakiyar. (Foot Mercato - in French)

Akwai yiwuwar Liverpool za ta sayarwa Barcelona da dan wasan tsakiyarta Georginio Wijnaldum wanda kwantiraginsa ke karewa da ƙungiyar a ƙarshen kakar wasanni da ake ciki.(Football Insider)

A wani labarin Barcelona za ta sayar da Philippe Coutinho don ta yi amfani da kudin wurin biyan Liverpool cikon kudin sayensa da ta yi a 2018. (Sport - in Spanish)

Su kuwa ƙungiyoyin Chelsea da Manchester City za suyi takarar sayen mai tsaron bayan Austria David Alaba, wanda kwantiraginsa da Bayern Munich na Jamus ke dab da ƙarewa.(Star on Sunday)

Rahotanni a Scotland na cewa tsohon ɗan wasan Manchester United Roy Keane ya nuna sha'awar jan ragamar Celtic, ƙungiyar da ya ritaya tare da ita. (Sun on Sunday)