Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 26Article 450432

BBC Hausa of Monday, 26 April 2021

Source: BBC

'Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 21 yayin da suka yi yunkurin sake kai hari a Geidam'

An kashe 'yan Boko Haram 21, da kuma karbe motar yakin da suka je da ita, inji rundunar sojoji An kashe 'yan Boko Haram 21, da kuma karbe motar yakin da suka je da ita, inji rundunar sojoji

Rahotanni daga jihar Yobe, da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun sake kai hari garin Geidam kwana guda bayan sun yi wa garin tsinke.

Majiyoyi sun ce ranar Asabar din nan ne mayakan suka sake shiga garin, inda suka shafe sa'o'i a suna artabu da sojojin Najeriya, har zuwa dare.

Majiyoyi sun shaida wa BBC Hausa cewa wasu mutanen da ke zaune a garin sun rika tserewa domin tsira da rayukansu yayin da lamarin ke faruwa.

Majiyoyin sun ce mayakan sun fasa shaguna da dama, kana suka yi awon gaba da kayan abinci mai yawa, kamar dai yadda suka yi lokacin da suka kai hari a ranar Juma'ar da ta gabata.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasa ta Najeriya Birgediya Janar Muhammed Yarima, ya bayyana wa BBC cewa 'yan Boko Haram din sun shiga cikin jama'a, don haka suna fuskantar matsala wajen gano su don yaki da su.

''Matsalar ita ce sun shiga cikin unguwanni, sai muka yi shawarar cewa a tsaya tukunna sai an kaɗa su waje, sai a far musu'' in ji kakakin rundunar sojin Najeriyar.

Ya ƙara da cewa sun yi nasarar kashe 'yan Boko Haram 21, da kuma karbe motar yakin da suka je da ita, da kuma ƙarin bindigogi takwas daga hannunsu.

Ranar Juma'a ne dai sojojin Najeriya da taimakon jirage masu saukar ungulu na rundunar sojin saman kasar, suka ce sun dakile wani harin 'yan kungiyar Boko Haram a garin na Geidam.

Wasu rahotanni sun ce mayakan na Boko Haram, sun mamaye garin a manyan motocin yaki, da zummar afka wa mutane yayin da suke shirin shan ruwa da yammacin wannan rana.

Majiyoyi sun kuma ce sama da maharan goma aka kashe, sakamakon ruwan bama-bamai da jiragen soji suka yi musu.

Majiyar ta fada wa jaridar PRNigeria cewa duk da cewa sojojin kasa sun fatattaki wasu 'yan ta'adda da suka gudu bayan an dakile harin, amma babu tabbacin ainihin adadin wadanda aka kashe daga cikinsu.