Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 27Article 450998

BBC Hausa of Thursday, 27 May 2021

Source: BBC

Shugabannin da aka buɗe wa ɗakin ƙabarin Manzon Allah a Madina

Firaministan Pakistan Imran Khan ɗakin da aka binne Manzon Allah a Madina Firaministan Pakistan Imran Khan ɗakin da aka binne Manzon Allah a Madina

Shugabanni da dama ne suka samu damar shiga ɗakin da aka binne Annabi Muhammadu (SAW), ɗaya daga cikin wurare mafi daraja a addinin Islama.

A farkon watan Mayun 2021 ne hukumomin Saudiyya suka bude wa Firaministan Pakistan Imran Khan ɗakin da aka binne Manzon Allah a Masallacnsa a Madina.

Imran Khan, ya kai ziyara masallacin ne kuma aka ba shi damar shiga har cikin ɗakin Nana Aisha (RA) ƙabarin Manzon Allah (SAW).

A cikin ɗakin akwai ƙaburburan Sahabansa, halifofin farko na Musulunci guda biyu, Abu Bakr RA da kuma da Umar RA.

BBC ta samu ƙarin bayani daga hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain kan shugabannin da suka taɓa samun damar shiga ɗakin Ƙabarin Manzon Allah (SAW)

Haramain Sharifain ya ce an buɗe wa shugabanni da dama da sarakunan Saudiyya, kuma ga shugabannin kamar yadda hukumomin na Saudiyya suka rubutowa BBC:

Shugabannin Pakistan

Paskitan na da alaƙa mai ƙarfi da Saudiyya, kuma ba Imran Khan ba ne shugaban Pakistan na farko da aka taɓa buɗe wa ɗakin da aka binne Annabi (SAW).

Tsohon Firaministan Pakistan Muhammad Nawaz Sharif wanda ya fi dadewa a kan mulki a tarihin ƙasar ya sha kai ziyara ƙabarin Manzon Allah a Madina.

Nawaz Sharif yana cikin shugabannin da hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya suka ce an buɗe wa ɗakin ƙabarin Manzon Allah (SAW).

Nawaz Sharif ya taɓa wallafa hotunansa a shafinsa na Twitter a ziyarar da ya kai Masallacin Manzon Allah a Madina a shekarar 2015 da 2018.

Haramain Sharifain ya ce an taɓa buɗe wa Firaminista Zulfikar Ali Bhutto ɗakin Manzo Allah wanda ya mulki Pakistan daga 1973 zuwa 1977.

Haka ma an buɗe wa Tsohon Firaminista Janar Muhammad Zia-ul-Haq wanda ya mulki Pakistan daga 1978 bayan hamɓarar da gwamnatin Ali Bhutto zuwa 1988 lokacin da ya mutu a hatsarin jirgin sama.

Shugaban Chechnya,Ramzan Kadyrov

Haramain Sharifain ya ce shugaban Jamhuriyyar Chechen Ramzan Kadyrov yana cikin shugabannin da aka taɓa buɗe wa ɗakin ƙabarin Manzon Allah.

Ramzan Kadyrov ya taɓa kai ziyara Masallacin Manzon Allah a Madina a 2018, inda ya samu tarba daga shugabannin Saudiyya.

Kadyrov wanda ya gaji mahaifinsa Akhmad Kadyrov da aka kashe a 2004, ya zama shugaban ƙasar Chechnya ne a 2007 bayan ya kai shekara 30 da haihuwa.

Sarakunan Saudiyya

Haramain Sharifain ya ce sarakunan Saudiyya da dama sun shiga ɗakin da aka binne Manzon Allah.

Hukumomin sun ce Sarki Abdulaziz da Sarki Faisal suna cikin kundin tarihi a rubuce da suka kai ziyara ɗakin da aka binne Manzon Allah.

Amma kuma Haramain Sharifain ya ce akwai sarakunan Saudiyya da suka kai ziyara da ba a rubuta su ba.

Shugaban Iran Sayyid Mohammad Khatami

Haramain Sharifain ya ce tsohon shugaban Iran Sayyid Mohammad Khatami na cikin shugabannin da aka ba damar shiga ɗakin da aka binne Manzon Allah.

Khatami mai sassaucin ra'ayi shi ne shugaban Iran na biyar wanda ya yi mulki daga 1997 zuwa 2005.

Ya yi ƙoƙarin samun goyon baya da haɗin kan ƙasashen larabawa a ziyarar mako ɗaya da ya kai wasu manyan ƙasashen yankin a 1998 ciki har da Saudiyya inda ya gudanar da aikin Umrah zamanin sarki Fahd.

Ziyarar da ya kai Saudiyya ita ce ta farko da wani babban jami'in gwamnatin Iran ya kai tun juyn juya halin ƙasar a 1979.