Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 17Article 450276

BBC Hausa of Saturday, 17 April 2021

Source: BBC

Shirin kare dajin Amazon na Brazil zai rika cin dala biliyan goma a shekara

Brazil za ta dauki matakan kare katafaren dajin Amazon mai albarkatu da kuma muhalli baki daya Brazil za ta dauki matakan kare katafaren dajin Amazon mai albarkatu da kuma muhalli baki daya

Gwamnatin Shugaba Bolsonaro na kokarin cimma wata yarjejeniya mai cike da takaddama da Amurka, wadda a bisa tanadinta, Brazil za ta dauki matakan kare katafaren dajin Amazon mai albarkatu da kuma muhalli baki daya, inda ita kuma za a saka mata da tallafi na kasashen waje.

Masu kare muhalli da kungiyoyi na cikin gida a Brazil na suka kan tanade-tanaden wannan yarjejeniya na sirri da gwamnatin Amurka ta Shugaba Biden ba tare da an baje komai a faifai ba, suna korafi da cewa ba a tuntube su ba.

Tun da farko mataimakin shugaban kasar ta Brazil Hamílton Mourão, ya ce kasarsa ta tsara cimma burin rage sare dazuka ba da izini ba da kashi goma sha biyar zuwa ashirin a shekara, ta yadda za a kawar da matsalar gaba daya zuwa shekara ta 2030.

Ya ce wannan bayani na kunshe ne a wata wasika da Shugaba Bolsonaro ya aika wa Shugaba Biden a makon nan da ke karewam, kafin taron koli na muhalli da za a yi a mako mai kamawa, wanda zai hada shugabannin duniya arba'in ta intanet.

An barnata murabba'in kilomita 11,088 na kurmin dajin na Amazon daga watan Agusta na 2019 zuwa watan Yuli na 2020, wanda hakan karin kashi tara da rabi ne bisa dari na barnar da aka yi a shekarar data gabata.

Dajin na Amazon wata muhimmiyar matattara ce da ke rage illar dumamar yanayi. Masana kimiyya sun ce barnar da ake yi wa dajin Amazon ta karu sosai tun lokacin da Jair Bolsonaro ya hau mulki a watan Janairu na 2019.

Shugaban na Brazil na karfafa wa mutane guiwa kan su yi noma da hakar ma'adanai a dajin da shi ne mafi girma a duniya mai dausayi. Akwai bishiyoyi da tsirrai da dabbobi iri daban-daban kusan miliyan uku da kuma mutanen yankin miliyan daya a wannan daji

Kafin taron na mako mai zuwa, a wani makamancinsa ta intanet din da ya hada shugabannin Faransa da Jamus, shugaban China, Xi Jinping ya nemi hadin kai wajen yaki da matsalar sauyin yanayi.

Mista Xi ya gaya wa Shugaba Macron na Faransa da Angela Merkel ta Jamus cewa wannan matsala aba ce da ta shafi duk wani mutum, wadda kuma ke bukatar hada hannu a gudu tare a tsira tare.

Kan haka shugaban na China ya nuna kin amincewarsa ga shirin kungiyar Tarayyar Turai na sanya haraji a kayan da aka samar a masana'antun da ke fitar da hayaki mai dumama yanayi sosai, wanda wannan haraji ne da zai shafi kayan da Chinar ke fitarwa waje.