Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 12Article 450748

BBC Hausa of Wednesday, 12 May 2021

Source: BBC

Sauye-sauyen da zan kawo a Darikar Tijjaniya – Muhammadu Sanusi na II

Tsohon Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II, sabon Khalifan ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya Tsohon Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II, sabon Khalifan ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya

Tsohon Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II, wanda aka naɗa sabon Khalifan ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya ya ce a shirye yake ya ga ya tunkari ƙalubalen da ɗariƙar ke fuskanta a wannan zamani.

Muhamamdu Sanusi II ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da ya yi da BBC inda ya jaddada cewa akwai matsaloli a ɓangarorin ilimi da aikin yi da haƙƙƙin iyali da abubuwan da suka shafi tsangaya da zawiyyowi musamman a arewacin Najeriya.

Ya ce zai mayar da hankali a waɗannan ɓangarori yadda ƴan ɗariƙa za su san cewa lallai ana ƙarni na 21.

"Su ma ƴan ɗariƙa Musulmi ne, don haka duk wasu matsaloli da Musulmi ke fuskanta a Najeriya su ma suna fuskanta," a cewarsa.

Khalifan na Tijjaniyya ya ce lokaci ya yi da miliyoyin ƴan ɗariƙa za su ƙarfafa kansu su yi ilimi mai zurfi yadda za a riƙa damawa da su a harkokin ƙasa kuma su bayar da gudunmowarsu ga ci gaban ƙasar.

Ya kuma ce zai yi amfani da wannan muƙami na Khalifan Tijjaniya wajen taimakawa Najeriya dangane da batun tsaro.

"Ɗariƙun sufaye dama mutane ne da kowa ya san su da son zaman lafiya da roƙon Allah, ba a samun mutane da su ke da tarbiyya irin ta ɗariƙa sun shiga harkokin ta'addanci," in ji tsohon sarkin na Kano

Don haka ya ce za a duƙufa roƙon Allah don neman sauƙi a matsalolin tsaro a Najeriya.

A watan Maris ɗin shekarar 2021 ne aka naɗa tsohon sarkin na Kano a matsayin jagoran ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya.

Khalifan Ibrahim Inyass ne ya jagoraci naɗa tsohon sarkin a matsayin Khalifa a babban taron ɗariƙar da aka gudanar a jihar Sakkwato.

Sarki Sanusi na II yanzu ya gaji kakansa Khalifan Tijjaniya na farko a Najeriya wato Sarki Muhammadu Sanusi I kuma ya ce ba shi da wani buri a rayuwa da ya wuce hawa kujerar kakan nasa.

Tun mutuwar marigayi Sheikh Isiyaka Rabiu a shekarar 2018 ba a naɗa sabon Khalifa ba a Najeriya.


Naɗin Sarki Muhammadu Sanusi II na biyu a matsayin Khalifan Tijjaniyya ya zo da ce-ce-ku-ce a Najeriyar inda wasu ɓangarorin Tijjaniyar suka ce ba su amince da naɗin nasa ba.

Wasu kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun ta ɗaukar labarai inda suka ambato Jagoran Ɗariƙar Tijjaniyya na duniya Mahi Nyass yana musanta naɗin Muhammadu Sanusi.

Mahi Nyass wanda ɗa ne kuma Khalifan Sheikh Ibrahim Nyass shi ne ke da alhakin naɗa jagoran Tijjaniyya a Najeriya da sauran sassan duniya kuma rahotannin sun bayyana cewa ya ce akwai hanyoyi da ake bi kafin a naɗa sabon Khalifa kuma yana ganin ba bi duka waɗannan hanyoyin ba kafin sanar da Muhamamdu Sanusi a matsayin jagoran na Najeriya.

Rahotannin sun ce Mahi Nyassa ya ce dole ne sai an shawarci manya-manyan Shehunnai kafin a yi sanarwar wadda shi zai sa wa hannu.

Haka kuma, an ambato shi yana cewa Muhammadu Sanusi bai nuna sha'awar zama jagoran Ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya ba kuma masu faɗa a ji a ɗariƙar ba su tsaida wanda suek ganin ya cancanta ba.

Sai dai a farkon wannan makon ne Muhammadu Sanusi II ya kai wata ziyara Kaolack a ƙasar Senegal, wato cibiyar Ɗariƙar Tijjaniyya ta duniya kuma mahaifar Shehu Ibrahim Nyass.

Sheikh Mahi Nyass ne ya tarbe shi kuma ya ayyana shi a matsayin jagoran Ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya.