Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 02Article 449442

BBC Hausa of Tuesday, 2 March 2021

Source: BBC

Real ta yi wasa na 100 a zagaye na biyu a Champions League test

LifeStyle test LifeStyle test

Real Madrid ta buga karawar Champions League ta 100 a fafatawar zagaye na biyu, inda ta doke Atalanta da ci 1-0 ranar Laraba.

Real ta ci Atalanta kwallo ta hannun Ferland Mendy saura minti hudu a tashi daga karawar.

Atalanta za ta ziyarci Real Madrid domin buga wasa na biyu ranar 16 ga watan Maris a Estadio Alfredo Di Stefano a Spaniya.

Madrid ta kawo wannan matakin ne a gasar bana, bayan da ta yi ta biyu a rukuni na biyu, kuma karon farko da za ta kara da Atalanta a gasar ta Champions League a tarihi.

    Barcelona ta kusa kamo Real Madrid Zidane ya bar Real Madrid
Daga 2010 zuwa 2019 Real kan kai matakin kusa da karshe, sai da a kaka biyu baya kungiyar ta kasa haura zagaye na biyu.

Hakan ya biyo bayan da Ajax da Manchester City suka yi waje da Real madrid a karawar zagaye na biyu a shekara biyu a jere kenan.

Cikin tarihin yawan lashe Champions League da Real ta kafa har da daukar hudu tsakanin 2014 zuwa 2018, kuma tana haduwa ne da manyan kungiyoyi a zagaye na biyu, amma ta kan taka rawar gani.