Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 05Article 450604

BBC Hausa of Wednesday, 5 May 2021

Source: BBC

Real Madrid za ta ziyarci Chelsea kwai da kwarkwata

Yan wasan kungiyar Real Madrid Yan wasan kungiyar Real Madrid

Kungiyar Chelsea za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu na daf da karshe a Champions League da za su fafata ranar Laraba a Stamford Bridge.

A wasan farko da suka kara a makon jiya ranar Talata, kungiyoyin sun tashi ne 1-1 a Spaniya.

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane zai je Ingila tare da fitattun 'yan wasa ciki har da Marcelo da Sergio Ramos da Federico Valverde da kuma Ferland Mendy.

A baya dai Real ta yi fama da 'yan wasa da ke jinya da hakan ke kawo mata koma baya na fuskantar wasa ba tare da cikakkun 'yan kwallonta ba.

Wasu lokutaun ta kan je karamar Madrid ta debo matasa wani karon har biyar ko shida, domin dai ta fita kunyar tamaula.

Sai dai kuma kungiyar ta Spaniya za ta buga wasan a Ingila ba tare da Raphael Varane ba, wanda ya yi rauni a karawar da Real ta doke Osasuna a gasar La Liga a karshen mako.

Kyaftin din Real, Sergio Ramos za a je da shi Ingila, kuma a karon farko da zai taka leda tun karshen watan Maris, sai dai ba a tabbas ko da shi za a fara karawar ko zai fara zaman benci.

Koda yake Eder Militao da Nacho na taka rawar gani a tsare bayan Real Madrid a rashin Ramos da Varane, sun kuma yi kokari da suka hana Liverpool cin kwallo a quarter final a Anfield.

Haka kum Zidane yana da zabi a gurbin masu tsaron baya daga hagu, bayan da Ferland Mendy ya murmure daga raunin da ya yi tun daga tsakiyar Afirilu.

Haka kuma dan kwallon Brazil, Mercelo zai bi Real zuwa Ingila domin buga wasa na biyu na daf da karshe, bayan da a baya ake ce zai yi aikin zabe a Spaniya.

Real din za ta je Stamford Bridge da Valverde, wanda bai buga wasanni ba a baya, sakamakon kamuwa da cutar korona.