Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 06 02Article 451110

BBC Hausa of Wednesday, 2 June 2021

Source: BBC

Real Madrid ta dauki Carlo Ancelotti a karo na biyu

Carlo Ancelotti sabon kocin Real Madrid Carlo Ancelotti sabon kocin Real Madrid

Real Madrid ta sanar ranar Talata cewar ta dauki Carlo Ancelotti a karo na biyu da zai ja ragamar kungiyar.

Dan kasar Italiya ya fara jan ragamar Real tsakanin 2013 zuwa 2015, wanda ya lashe Champions League a kakarsa ta farko a kungiyar.

Ancelotti zai maye gurbin Zinedine Zidane wanda ya ajiye aikin cikin watan nan, bayan da Real Madrid ba ta lashe kofi ba a 2020/21.