Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 26Article 450428

BBC Hausa of Monday, 26 April 2021

Source: BBC

Ranar maleriya ta duniya: Wasu kasashe za su ga bayan cutar

Ko wani Afrilu 25 ne ranar duniya ta yaki da cutar zazzabin cizon sauro Ko wani Afrilu 25 ne ranar duniya ta yaki da cutar zazzabin cizon sauro

Yau take ranar duniya ta yaki da cutar zazzabin cizon sauro, wato maleriya, a don haka ne hukumar lafiya ta duniya, WHO ke kira da a kara zage damtse wajen gwanin bayan cutar, wadda har yanzu take hallaka rayuka sama da dubu dari hudu, yawancinsu yara 'yan kasa da shekara biyar, a duk shekara.

Hukumar ta ce duk da kalubalen da ke tattare da annobar, akalla kasashe ashirin da biyar, wadanda suka hada da Botswana da Thailand da kuma Afirka ta Kudu suna da damar iya kawar da cutar ta zazzabin cizon sauro nan da shekara biyar.

Ranar ta 25 ga watan Afrilu, da ke zaman ranar duniya ta neman ganin karshen cutar ta zazzabin cizon sauron, a bana ta zo a yayin da harkokin kula da lafiya a kasashen duniya ke cikin mawuyacin hali wanda annobar korona ta haddasa.

Kashi daya bi sa uku na kasashen da cutar ta maleriya ta addabe su, sun bayar da rahoton cewa a cikin shekarar da ta gabata ayyukansu na yaki da cutar; kare ta da kuma maganinta sun gamu da cikas.

Dokar kullen korona ta sa an samu jinkiri wajen kai gidan sauro, wasu masu fama da cutar ta maleriya sun rasa maganinsu, saboda ba su iya zuwa cibiyoyi ko asibitocin da ake musu magani ba.

To amma duk da wannan annobar ta korona, kasashe da yawa sun ci gaba da samun nasara ta kokarin kawar da cutar ta maleriya. Wasu kamar Algeria da Iran da Malaysia, ba su bayar da rahoton wasu 'yan cikin kasar da suka kamu da cutar ba a shekarar da ta gabata, yayin da wasu kamar su Bhutan da Costa Rica da kuma Nepal suka bayar da rahoton mutane kasa da dari daya da cutar ta kama.

Da wannan a yanzu hukumar lafiya ta duniya ta sanya burin samar da karin kasashe ashirin da biyar da take ganin ba za a sake samun masu kamuwa da maleriyar ba zuwa shekara ta 2025.

Ana ganin ko da wane irin kalubale ne ko matsalolin kula da lafiya ake fuskanta, bai kamata a yi sako-sako ko sassauta yunkurin raba duniya da cutar da ke kashe rayuka sama da dubu dari hudu ba, a shekara wadanda kuma yawancinsu kananan yara ne.

A cigaban da aka samu ta wannan yaki a kwanakin nan aka bayyana allurar riga-kafin cutar zazzabin cizon sauron da masana suka kirkiro a Jami'ar Oxford ta Birtaniya, cewa an samu nasarar kashi 77 cikin dari na inganci a gwaje-gwajen da aka yi a kasar Burkina Faso.

Sakamakon ya nuna cewa ruwan allurar na da matukar inganci fiye da ainihin ruwan riga-kafin cutar ta maleriya daya kadai da ake da shi.

Wannan ya sa za a fadada gwajin inda za a yi shi sosai da sosai a kan kananan yara kusan dubu biyar a fadin kasashen Afirka.

Masanan sun ce ruwan riga-kafin ya nuna matukar inganci a gwaje-gwajen, wanda akwai tabbacin yiwuwar rage yawan wadanda cutar ke kashewa a duk shekara.