Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 04Article 449461

BBC Hausa of Thursday, 4 March 2021

Source: BBC

Premier League: Man City ta bai wa Man United tazarar maki 14

Cocin Man United Ole Gunnar Solsksjear Cocin Man United Ole Gunnar Solsksjear

Manchester United ta tashi wasa ba ci 0-0 a gidan Crystal Palace a fafatawar Premier League da suka gwabza ranar Laraba.

Da wannan sakamakon City wadda take ta daya a kan teburi da maki 65, ta bai wa United tazarar maki 14 kawo yanzu.

Palace da United sun kara a gasar Premier ranar 19 ga watan Satumba a wasan farko, inda Palace ta doke United da ci 3-1 a Old Trafford.

Har yanzu United ba ta yi rashin nasara ba a wasannin waje a gasar Premier League a bana ba, wadda cikin karawa 21 ta ci fafatawa 13 da zanjaras takwas.

United ta ci wasa tara daga 12 data buga a tsakiyar mako a Premier League, ciki har da lashe dukkan karawa shida da ta yi a waje.

Ita kuwa Crystal Palace tana ta 13 a kasan teburin Premier League da makinta 34.

Ranar 7 ga watan Maris, Manchester United za ta ziyarci Manchester City a Etihad a wasan na Premier League.

A kuma ranar Tottenham za ta karbi bakuncin Crystal Palace.