Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 27Article 450983

BBC Hausa of Thursday, 27 May 2021

Source: BBC

Nigeria za ta gudanar da gasar tsalle-tsalle da guje-guje

Za a yi wasannin ne tsakanin 23 zuwa 27 ga watan Yuni Za a yi wasannin ne tsakanin 23 zuwa 27 ga watan Yuni

Ministan Matasa da bunkasa wasanni na Najeriya, Sunday Dare ya bugi kirjin karbar bakuncin gasar tsalle-tsalle da guje-guje ta Afirka da za a yi a Legas a watan gobe.

Tun farko an tsara cewar Algeria ce za ta karbi bakuncin wasannin, daga baya ta bukaci a dage gasar, sakamakon barazanar da cutar korona ke kara yi a fadin duniya.

Za a yi wasannin ne tsakanin 23 zuwa 27 ga watan Yuni a Najeriya, domin tantance wadanda za su wakilci nahiyar a gasar Olympic da birnin Tokyo zai karbi bakunci a bana.

An tsayar da ranar karshe ta 29 ga watan Yuni domin tantance wadanda za su wakilci nahiyar Afirka.

Dare da shugaban wasan tsalle-tsalle na Afirka, Kalkaba Malboum sun tattauna a Masar ranar Litinin kan yadda za a gudanar da wasannin a filin Teslim Balogun a Legas cikin nasara.

Karo na uku ana dakatar da wasannin kafin daga baya Najeriya ta amince a gudanar da gasar a kasarsa, bayan da tun cikin 2020 ya kamata a fafata amma cutar korona ta kai tsaiko.

A baya an tsara yin wasannin a Algeria a birnin Oran tsakanin 1 zuwa 5 ga watan Yunin 2021 daga baya aka mayar da karawar Algeria tsakanin 22 zuwa 26 ga watan Yuni.