Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 28Article 450469

BBC Hausa of Wednesday, 28 April 2021

Source: BBC

Nagelsmann zai karbi aikin kocin Bayern Munich

Kocin RB Leipzig, Julian Nagelsmann zai koma horar da Bayern Munich daga badi Kocin RB Leipzig, Julian Nagelsmann zai koma horar da Bayern Munich daga badi

Kocin RB Leipzig, Julian Nagelsmann zai koma horar da Bayern Munich daga badi zuwa kaka biyar, kamar yadda kungiyar ta Jamus ta sanar.

Wanda ke jan ragamar kungiyar a yanzu haka Hansi Flick ya sanar cewar zai bar Bayern Munich a karshen kakar bana.

Mai shekara 33, Nagelsmann daya ne daga cikin fitattun matasan kociyoyin da ake ji da su a Turai, wanda ya kai Leipzig wasan daf da karshe a Champions League a bara.

Kocin dan kasar Jamus wanda zai karbi jan ragamar Munich daga 1 ga watan Yulin bana, zai sa Bayern ta biya rarar kudi da ya kai fam miliyan 20 ga Leipzig.

Nagelsmann ya zama matashin mai horar da tamaula a tarihin Bundesliga mai shekara 28 a lokacin da ya ja ragamar Hoffenheim a Fabrairun 2016.

Bayan da ya koma Leipzig a 2019 ya kai kungiyar mataki na uku a gasar Bundesliga da karawar daf da karshe a Champins League a kakarsa ta farko.

Leipzig tana mataki na biyu a gasar Bundesliga da tazarar maki bakwai tsakaninta da Wolfsburg ta uku kuma saura karawa uku-uku a karkare gasar Jamus ta bana.