Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 06 04Article 451144

BBC Hausa of Friday, 4 June 2021

Source: BBC

Naftali Bennett: Tarihin dan siyasa da ke shirin zai zama sabon firaiministan Isra'ila

Naftali Bennett, dan siyasa da ke daf da zama firaiministan Isra'ila Naftali Bennett, dan siyasa da ke daf da zama firaiministan Isra'ila

Naftali Bennett, wanda ake sa ran zai zama firaiministan Isra'ila, bayan jam'iyyun hamayya sun amince su kafa sabuwar gwamnatin da za ta kawo karshen mulkin Benjamin Netanyahu na shekara 12, tsohon babban kwamandan soja ne kuma attajiri wanda ya ce ba zai goyi da bayan kafa kasar Falasdinu ba.

Mista Bennett ya dade yana fatan zama firaiminista, kuma jam'iyarsa ta Yamini mai ra'ayin rikau ta samu galaba da kujeru kalilan a zaben da aka gudanar a baya.

Duk da cewa bangarensa ya zo na biyar da kujerun majalisa bakwai, Mista Bennett ya samu karin matsayi na mai nada mukamai.

Naftali Bennett, mai shekaru 49, tsohon na hannun daman Mista Netanyahu ne, wanda ya yi aiki a matsayin shugaban ma'aikatan gwamnatinsa daga shekarar 2006 zuwa 2008. Ya fice daga jam'iyar Likud ta Mista Netanyahu ta shiga jami'iyar Jewish Home, ya kuma zama dan majalisar dokoki bayan da ya kai ta ga nasara a zaben shekarar 2013.

Ya ci gaba da kasancewa minista a ko wace gwamnatin hadaka har ya zuwa shekarar 2019, bayan da sabuwar jam'iyyar gamayyar da ya kafa ta New Right ta gaza cin ko da kujera daya a zaben waccan shekarar. Watanni 11 bayan nan ne Mista Bennett ya sake komawa majalisar dokoki a matsayin jagoran jam'iyar Yamina.

Ana yawan bayyana shi a matsayin wanda "ya fi Mista Netanyahu zama dan ra'ayin rikau," Naftali Bennett gwanin iya magana ne a fagen wayar da kan jama'a kan kasancewar Isra'ila a matsayin kasar Yahuduwa da kuma ikirarin Yahudawa kan tarihi da addini kan yankin Gabar Yamma ta Kogin Jordan, da Gabashin Kudus da Tuddan Golan na kasar Syria - yankin da Isra'ila ta mamaye a shekarar 1967.

Ya dade da shigewa gaba wajen fafutikar 'yancin zaman Yahudawa a yankin Gabar Yamma ta Kogin Jordan (ya taba zama shugaban majalisar Yesha, wakilin Yahudawa mazauna yankin), duk da kuwa ya bayyana cewa Isra'ila ba ta da iko a kan Gaza (inda Isra'ila ta janye dakarunta ta mazauna a can a shekarar 2005).

Yahudawa fiye da dubu 600,000 ne ke zaune a matsugunai kusan 140 a yankin Gabar Yamma ta Kogin Jordan da Gabashin Kudus, da kasashen duniya ke dauka a matsayin haramtacce, duk da cewa Isra'ila ta ki amincewa da hakan.

Makomar mazauna yankin na daya daga cikin abubuwan da ake fi yin ce-ce-ku-ce a kansa tsakanin Isra'ila da Falasdinawa, da suka bukaci ficewarsu, kana a kafa kasa mai cin gashin kanta a Gabar Yamma ta Kogin Jordan da kuma Gaza, kana Gabashin Kudus ya kasance babban birnin kasar.

Mista Bennett, wanda ke magana da harshen turanci sosai, ya bayyana a kafofin talabijin na kasashen waje yana kare matakan Isra'ila.

Yayin da yake magana gaba-gadi kana cikin nuna isa, a wata muhawarar kafar talabijin ta Isra'ila, ya taba nuna yatsa ga wani dan majalisa Balaraben Isra'ila kan furta cewa Yahudawa ba su da 'yancin zama a Gabar Yamma ta Kogin Jordan, ya fada masa cewa: "Tun lokacin kana lilo a tsakanin bishiyoyi, muke da kasar Isra'ila a nan."

Mista Bennett ya yi watsi da batun kirkiro kasar Falasdinu tare da Isra'ila - matakin da aka bayyana cewa zai warware matsalolin rikicin kasashen biyu, wanda kasashen duniya da suka hada da shugaban Amurka Joe Biden ke bukata.

"Muddin ina da duk wani karfin iko, ba zan taba amincewa na mika ko da taku daya na kasar Isra'ila ba. Fakat," ya bayyana hakan a wata tattaunawa da shi cikin watan Fabrairun shekarar 2021.

A maimakon haka, Mista Bennett ya bukaci kara kaimin Isra'ila wajen rike yankin Gabar Yamma ta Kogin Jordan.

Mista Bennett ya kuma dauki tsattsauran mataki kan barazanar mayakan Falasdinawa wadanda ya ce yana goyon bayan hukuncin kisa a kansu.

Ba a taba amfani da hakan ba a Isra'ila baya ga na Adolf Eichmann, dan Nazi wanda shi ne kashin bayan kisan kare dangin da aka yi lokacin yakin duniya na biyu, wanda kuma aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 1961.

Ya nuna rashin goyon baya ga yarjejeniya da shugabannin kungiyar Hamas ta gaza da ya haddasa barkewar fada a shekarar 2018, kana ta zargi kungiyar da kisan daruruwan fararen hularsu a hare-hare ta saman Isra'ila da ta yi a matsayin mayar da martani kan hare-haren rokokin da aka kai mata daa Gaza a sabon rikicin da ya barke a sekarar 2021.

A yakin neman zaben shekarar 2014, ya kalubalanci jaridar New York Times da ta Haaretz ta Isra'ila kan sukar lamirin matakin Isra'il.

Mista Bennett ya yi aiki a rassa biyu na dakarun musamman na kasar Isra'ila a lokacin ayyukan sojin sa, kafin ya kafa kamfaninsa na kayan lataroni, da ya sa ya zama hamshakin attajiri.

Yayin da yake magana game da attajirancinsa a wata tattaunawa da shi a shekarar 2014, ya bayyana cewa: "Ba na cin naman tozo 17, kana ba ni da jirgin sama ko jirgin ruwa. Hakan ya sa na samu 'yancin yin abin da na ga dama."