Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 15Article 449666

BBC Hausa of Monday, 15 March 2021

Source: BBC

Mayakan Boko Haram 'sun kashe sojojin Najeriya kusan 30 a kwana huɗu'

Mayakan kungiyar Boko Haram Mayakan kungiyar Boko Haram

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya kusan 30 a hare-haren da suka kai a arewa maso gabashin kasar cikin kwana hudu, a cewar majiyoyi daga rundunar soji da kuma fararen hula.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters, wanda ya ambato wadannan majiyoyi suna tabbatar masa da labarin, ya kara da cewa hare-haren sun faru ne tun daga Larabar makon jiya.

Matsalolin tabarbarewar tsaro na ci gaba da ta'azzara a Najeriya a watannin baya-bayan nan, ciki har da hare-haren da ke faruwa a raewa maso gabashin kasar.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Reuters cewa hare-hare guda hudu sun yi sanadin mutuwar akalla sojoji 27 da kuma 'yan kato-da-gora 10 na rundunar Civilian Joint Task Force (CJTF), ciki har da shugaban wani yanki na rundunar.

Mayakan na kato-da-gora sun dade suna hada gwiwa da jami'an tsaro wajen fafarar 'yan kungiyar Boko Haram da suka addabi yankunansu.

Masu magana da yawun rundunar sojin kasa ta Najeriya da na rundunar tsaron kasar ba su dauki kiran wayoyin da Reuters ya yi musu ba da ma sakon text da aka aika musu a kan batun.

Mayakan kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP), sun yi ikirarin kai hari a garin Monguno Ranar Juma'ar da ta gabata cikin sakon da suka fitar a kamfanin labarai na Amaq news agency ranar Asabar.

ISWAP ta ce ta kashe sojoji guda 33 sannan ta kama daya. Majiyoyin soji guda biyu da kuma wani mayakin CJTF sun ce harin, wanda aka kai tsakanin Monguno da Kukawa, ya yi sanadin mutuwar soja 11 zuwa 15, yayin da wasu da dama daga cikinsu suka bata.

Kazalika, an kashe 'yan kato-da-gora hudu, in ji majiyoyin.

Sun kara da cewa sojoji sun kashe mayakan Boko Haram takwas a fafatawar da suka yi a garin Gamdu ranar Laraba.

Yakin da gwamnatin Najeriya ta kwashe fiye da shekara 10 tana yi da Boko Haram da kuma ISWAP, ɓangaren ƙungiyar da ya balle a 2016, ya raba mutum fiye da miliyan biyu da muhallansu yayin da ya yi sanadin mutuwar mutum 36,000.