Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 12Article 449616

BBC Hausa of Friday, 12 March 2021

Source: BBC

Matsalar Tsaro: Buhari ya bai wa hafsoshin tsaron Najeriya wa’adin mako 6

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce gwamnati ba za ta yi sassauci ga masu ɗaukar bindiga suna kashe-kashe ba.

Ya kuma jaddada umarnin da ya bayar a baya-bayan nan cewa duk wani wanda ba jami'in tsaro ba aka kama shi da manyan makamai irin bindigar nan ta AK 47 a harbe shi.

Shugaba Buharin ya yi mamakin duk da cewa ba a daɗe da sake bude iyakokin ƙasar ba amma yan bindigar ba sa rashin makamai.

    'Yan bindiga sun kashe mutum 937 a Jihar Kaduna a 2020 'Dalilin da ya sa muka rufe dukkan makarantu a Jihar Neja'
Game da haka ne shugaban kasar Najeriyar ya ce ya ɗebar wa sababbin shugabannin tsaro daya naɗa mako shida ya ga sauyi a kasa.

Muhammadu Buhari ya ce ba zai yiwu damina ta faɗi mutane ba za su iya shiga gona su yi noma ba.

Sarakunan gargajiyar ƙsar ne suka kai kuka game da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar, sai dai wasu na ganin jami'an tsaro za su fuskanci ƙalubale musamman idan aka dubi cewa wannan yaƙi ne na sari ka noƙe.