Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 27Article 450997

BBC Hausa of Thursday, 27 May 2021

Source: BBC

Matar da ta yi tafiyar kilomita 16,000 don kamo malam buɗe mana littafi

Sara ta ce a kodayaushe tana samun mutanen da za su taimaka wa malam buɗe mana littafi Sara ta ce a kodayaushe tana samun mutanen da za su taimaka wa malam buɗe mana littafi

Yaya karamin kwaro wanda bai kai nauyin giram daya ba - wanda yake da mitsitsiyar kwakwalwa - yake tafiyar dubban kilomitoci?*

Wannan yana daya daga cikin abubuwan al'ajabi game da rayuwar kwari: miliyoyin malam buɗe mana littafi da ke tashi kowacce shekara daga inda ake kyankyashe su a Amurka zuwa Canada sannan bayan sun soma tafiya daga wasu yankunan tsakiyar Mexico a lokacin hunturu, kuma suna komawa can a lokacin bazara. Sai dai yawansu yana raguwa.

Wata mata da take son daukar mataki a kan wannan raguwa da kwarin suke yi ita ce masaniya kan harkar ilimi da kuma alkinta muhalli Sara Dykman, kuma ta san yadda kaurar malam buɗe mana littafi take faruwa - ita ma ta taba yin kaurar.

Abin ya zama labari

Sara tana so ta karfafa gwiwar yara domin su alkinta malam buɗe mana littafi, amma sai ta bullo da hanya mai cike da hikima ta bayar da wannan labari.

"Za mu iya kwashe tsawon rana muna lissafa gaskiyar lamura. Amma ba za ka manta haduwa da mutumin da ya yi doguwar tafiya, wanda ya kwana a bayan gidanka da kuma wanda ya ziyarci lambunka," in ji Sara a hirarta da BBC.

A kokarinta na isar da sakon ita kanta ta zama labari: a 2017 ta kasance mutum na farko da ta yi tafiya a kan keke inda ta bi hnayoyin da malam buɗe mana littafi suke wucewa - ta kwashe kilomita 16,417 tana tafiya.

A kwanakin baya ne Sara ta wallafa littafi a kan yadda ta yi tafiya a kan keke sannan ta yi magana da BBC a kan abin da ya karfafa mata gwiwar yin hakan.

"Ina bukatar fiye da abinci da ruwa da iskar oxygen domin na rayu. Ina bukatar abin mamaki."

Tafiya mai muhimmanci

Sara ta soma balaguronta a kan keke ne daga tsakiyar Mexico. Ta hau kan tsaunuka inda ta ga dubban malam buɗe mana littafi cakude wuri guda, suna riji a kan rassan bishiya.

"A Mexico, malam buɗe mana littafi suna kwashe tsawon lokacin hunturu a cikin daji mai fadin kafa 10,000 (3,050m) da ke saman ruwan teku. Yanayi ne mai kyawu da ba shi da zafi ko kuma sanyi sosai, " a cewar Sara.

Zuwan bazara kan bai wa malam buɗe mana littafi damar yin balaguro mai nisa.

Suna soma tafiya arewa ne inda suke tashi su bi ta tsaunukan Sierra Madre mountains. Bayan sun shiga Amurka, malam buɗe mana littafi suna warwatsuwa domin yankuna masu yawa.

Sara ta bi su ta hanyar amfani da taswirar Google maps da hanyoyi da masu bincike suna fitar, sai dai a wasu lokutan tana kaucewa daga kan hanya domin ta samu ta cimma malam buɗe mana littafin.

Duk da haka tana jin dadin yadda take tafiya a kan keke.

"Tuka keke abu ne mai dadi: za ka iya isa wuri ba tare da bata lokaci mai yawa sanna za ka ji cewa kana samun ci gaba. Kuma za ka iya hawa kan tsaunuka da samu abubuwa da dama."

Ta gyara kekenta da ta saya a 1989 ta yadda zai dauki abinci da ruwa da tanti - kusan nauyin kilogiram 30 baki daya.

Lokacin da ta yi tafiyar, mutane da dama sun karrama ta a gidansu. Ta ji dadin zama a gidan gonarsu da cocinsu.

Gabatar da sako

Tsawon lokacin balaguron da ta yi ta rika sauka daga kan keke ta tattauna da yara 'yan makaranta.

Sara tana kallon malam buɗe mana littafi a matsayin wakilan kwari na duniya.

"Za ka soma da malam buɗe mana littafi sannan ka ga sauran kwari a cikin lambuna. Gizo-gizo da sauran kwari suna nuna irin kyawun komai."

Sara ta yi misalai da abubuwan da ta fahimta a tafiyar da ta yi wajen fahimtar da daliban kan yanayi da alkinta muhalli.

She lissafa cewa ta yi magana da fiye da dalibai 9,000 kai tsaye, kuma shekaru hudu bayan haka, ta ce har yanzu tana ganawa da wasunsu.

Daya daga cikin 'yan matan da Sara ta gana da su a 2017 yanzu ta soma noman lambu a makarantarsu wanda zai sa su alkinta malam buɗe mana littafi.

Tsarin abinci

Baya ga kyawu da kuma jin dadin da suke sanya wa mutane, Sara ta bayyana rawar da malam buɗe mana littafi ke takawa wajen hada barbara tsakanin furanni, lamarin da ke samar da abincin da muke ci.

Kazalika suna taka rawa wajen gudanar da rayuwar sauran kwari da tsuntsaye.

"Macen malam buɗe mana littafi tana yin kwaikwaye 500, kuma kashi daya daga cikinsu yana kai wa matakin balaga. Sauran kwaikwaye 495 suna bayar da gudunmawa wajen samar da abinci ga sauran," in ji ta.

Sauyin yanayi yana iya yin tasiri a rayuwar malam buɗe mana littafi, domin kuwa yanayin jikinsu yana dacewa da wurin da suke zama.

Cincirindon malam buɗe mana littafi da ke soma tafiya daga Mexico yana soma to raguwa idan suka shiga Amurka. Daga bisani sauran suna zama a ko ina tsakanin mako biyu zuwa biyar, don haka rukuni na uku da na hudu da kuma na biyar ne yake isa Canada da kuma arewacin Amurka.