Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 06Article 450640

BBC Hausa of Thursday, 6 May 2021

Source: BBC

Manyan hafsoshin tsaro da 'yan Majalisar Dattijan Najeriya na ganawa kan rashin tsaro

Shugabannin tsaron Najeriya a wani taro a fadar Shugaban kasa a Abuja Shugabannin tsaron Najeriya a wani taro a fadar Shugaban kasa a Abuja

Shugabannin tsaron Najeriya da na 'yan Majalisar Dattijan Najeriya na tattaunawar sirri a zauren majalisar dokokin kasar da ke Abuja.

Hafsoshin tsaron na amsa gayyatar 'yan majalisar ce domin bayyana musu halin da ake ciki game da taɓarɓarewar tsaro a faɗin ƙasar.

Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar Leo Irabor ne ya jagoranci hafsoshin tsaron zuwa majalisar, inda Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya karɓe su, kamar yadda majalisar ta wallafa a shafinta na Twitter:



Sauran jami'an da ke amsa gayyatar sun haɗa da da shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA da kuma na shugaban hukumar tsaron farin kaya wato DSS.

Bayan Sanata Ahmad Lawan ya gode musu bisa ayyukan kare tsaron ƙasa a madadin majalisar sai suka shiga tattaunawar sirri da misalin ƙarfe 11:21.

Suna wannan ganawa ne a yayin da Najeriya take ci gaba da fama da matsalolin tsaro daga kowacce kusurwa ta ƙasar.

A arewa maso yammacin kasar ana ci gaba da fama da matsalolin masu garkuwa da mutane da 'yan fashin daji, wadanda suke kashe mutane ko kuma su tilasta musu biyan kudin fansa.

Wannan matsala ta fi ƙamari a jihohin Kaduna da Zamfara da Neja da kuma Katsina.

Alkaluma sun nuna cewa an sace dalibai fiye da 800 daga watan Disamba zuwa yanzu.

Buhari ya gaza?

Kazalika mayakan kungiyar Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a arewa maso gabashin kasar, ciki har da wadanda suke kai wa a kan sojoji.

A baya bayan nan rahotanni sun nuna cewa sojoji fiye da talamin ne suka mutu sakamakon harin na mayakan Boko Haram da farmaki bisa kuskure da sojin sama suka kai a sansaninsu da ke Mainok a jihar Borno.

Sai kuma tashe-tashen hankulan da ke ci gaba da ta'azzara a kudu maso gabashin Najeriya wanda ake zargin masu fafutukar ɓalllewa daga kasar na kungiyar IPOB ne suke kitsa su.

Hukumomi sun zarge su da kai hare-haren kan ofisoshin 'yan sanda da kubutar da daurarrun da ke gidajen yari a jihar Imo da ma wasu jihohi na yankin.

Wadannan kalubalen tsaro na cikin dalilan da suka sanya mutane da dama suke ganin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gaza inda wasu ke kira a gare shi da ya sauka daga mulki.

Sai dai shugaban kasar ya dage cewa yana yin bakin kokarinsa, yana mai cewa nan ba da jimawa ba za su shawo kan lamarin.

A farkon makon nan fadar shugaban kasar ta yi zargin cewa wasu malaman addini da tsoffin masu rike da mukamai na siyasa na son jefa kasar cikin rikici domin su yi amfani da damar wajen kifar da gwamnatinsa.

Sai dai masu sharhi sun ce wannan zargi takmar neman kawar da hankulan 'yan kasar ne daga manyan kalubalen da gwamnati ta kasa magancewa.