Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 17Article 450833

BBC Hausa of Monday, 17 May 2021

Source: BBC

Mancini zai ci gaba da horar da Italiya zuwa 2026

Roberto Mancini, kocin tawagar kwallon kafa ta Italiya Roberto Mancini, kocin tawagar kwallon kafa ta Italiya

Roberto Mancini ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da horar da tawagar kwallon kafa ta Italiya zuwa karshen kakar 2026.

Shugaban hukumar kwallon kasar Italiya, Gabriele Gravina ne ya sanar da hakan ranar Litinin.

Tun farko kwantiragin Mancini zai kare a karshen gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022, yanzu kuma sai bayan ta 2026 zai karkare.

Hukumar kwallon kafar Italiya ta bai wa Mancini aikin jan ragamar tawagar a Mayun 2018, bayan da ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya da aka yi a Rasha.

Mai shekara 56 ya ja ragamar wasa 28 ya ci 19 da rashin nasara biyu, inda ya kai Italiya gasar kofin nahiyar Turai duk da saura wasa uku suka rage a lokacin.

Haka kuma ya kai kasar karawar daf da karshe a UEFA Nations League, inda zai fuskanci Spaniya cikin watan Oktoba.

Tawagar Italiya tana rukunin farko tare da Turkiya da Wales da kuma Switzerlad a gasar nahiyar Turai da za a fara daga 11 ga watan Yuni zuwa 11 ga watan Yuli.

Haka kuma Italiya za ta karbi bakuncin wasanta na farko da Turkiya inda za su kara a birnin Rum a gasar ta cin kofin nahiyar Turai da ya kamata a buga tun bara, amma cutar korona ta kai tsaiko.