Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 06Article 450634

BBC Hausa of Thursday, 6 May 2021

Source: BBC

Manchester United za ta buga wasa hudu a kwana takwas

Manchester United za ta buga wasa hudu a kwana takwas Manchester United za ta buga wasa hudu a kwana takwas

An tsayar da ranar Alhamis 13 ga watan Mayu, domin buga wasan Premier League na ranar Lahadi da aka dage tsakanin Manchester United da Liverpool a Old Trafford.

Hakan na nufin United za ta buga karawa biyu kenan cikin awa 50, bayan da wasan da kungiyar za ta kara da Leicester City aka tura shi zuwa ranar 11 ga watan Mayu.

Wasan Liverpool da West Brom wanda aka yi tsammani za a dage yana nan kamar yadda aka tsara tun farko da za su fafata ranar 16 ga watan Mayu.

Dubban magoya bayan United ne suka yi zanga-zanga kan kin iyalan Glazer masu kungiyar a Old Traford da kuma Otal din 'yan wasa tun kan karawar ranar Lahadi.

Wasan na Premier League da ba a buga ba ranar Lahadi shi ne Premier League na farko da ba a yi ba, sakamakon zanga-zangar magoya baya.

Duk da rade-radin cewar magoya baya za su kalubalancin kungiyar a shirinta na zuwa Italiya da za ta yi, 'yan wasa sun isa filin jirgin sama don zuwa Roma wasa na biyu na daf da karshe a Europa League ba tare da wani abu ya faru ba na tashin hankali.

Duk da wasan Roma da United za ta buga ya hada da wanda za ta je Aston Villa ranar Lahadi a gasar Premier da na Leicester ranar Talata da na Liverpool ranar Alhamis duk cikin kwana takwas.