Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 10Article 450138

BBC Hausa of Saturday, 10 April 2021

Source: BBC

Man United ta gwada wa Granada kwanji a Europa

Yan wasan kungiyar Manchester United Yan wasan kungiyar Manchester United

Manchester United ta dauki hanyar kai wa wasan daf da karshe a Europa League, bayan da ta je ta doke Granada 2-0 ranar Alhamis.

Marcus Rashford ne ya fara ci wa United kwallo, bayan da ya samu tamaula daga Victor Lindelof, ya kuma buga ta wuce mai tsaron raga, Rui Silva.

Yangel Herrera mai buga wasannin aro daga Manchester City ya kai wa United hari daga wajen da'ira ta 18, amma kwallon ya bugi turke.

Shima tsohon dan wasan Tottenham, Roberto Soldado ya samu wata dama mai kyau, amma da ya buga kwallon sai ta yi fadi ta fita waje.

United ta ci kwallo na biyu a bugun fenariti ta hannun Bruno Fernandes, bayan da Yan Brice ya yi wa dan kwallon Portugal din keta a da'ira ta 16.

United za ta karbi bakuncin wasa na biyu a Old Trafford ranar Alhamis, kuma duk wadda ta kai wasan daf da karshe za ta kece raini tsakanin Ajax ko kuma Roma.

Kungiyar ta Old Traford ta yi rashin nasara a wasa daya daga 17 da ta yi a dukkan karawa, za kuma ta ziyarci Tottenham a gasar Premier ranar Lahadi.