Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 19Article 450293

BBC Hausa of Monday, 19 April 2021

Source: BBC

Sojojin Najeriya sun haramta zirga-zirga a hanyar Damaturu

Hoton sojojin Najeriya Hoton sojojin Najeriya

Sojojin Najeriya sun hana zirga-zirga a hanyar Damaturu-Damboa-Biu biyo bayan hare-haren da mayaƙan ƙungiyar ISWAP/Boko Haram suka kai kan sansanin sojin da ke Kumuya a jihar Yobe.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta tattaro bayyanan da ke cewa ƴan ta'addan sun kai harin ne lokacin da sojojin da aka girka a Buni Gari suka tafi aikin sintiri.

'Yan ta'addan wadanda wasu suka taimaka musu da bayannai sun kutsa kai cikin yankin na Kumuya, tare da afkawa ƙauyuka da sansanin sojoji kuma suka lalata kayan sojoji masu yawa.

A lokacin harin, mayakan sun yi amfani da manyan makamai wajen lalata kayan sojoji tare da yin sintiri a cikin al'umma don hana sojoji sake ƙarfafa kansu.

Amma duk da haka, sojojin da ke kasa sun zo sun yi artabu da su.

Daga karshe sojojin Najeriya da suka hada ƙarfi da ƙarfe sun fatattaki maharan.

Duk da cewa an samu labarin cewa wani ɓangare na sansanin sojoji da ke Kumuya ya kone yayin harin, amma kafar watsa labarai ta PRNigeria ba ta iya tabbatar da adadin sojojin da suka hallaka ba.