Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 11Article 449586

BBC Hausa of Thursday, 11 March 2021

Source: BBC

'Kudin Ibori na al'ummar jihar Dellta ne'

Tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori Tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori

Majalisar wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta damƙa wa jihar Delta kuɗin almundahanar James Ibori da Burtaniya ke shirin mayar wa ƙasar, da yawansu ya kai fam miliyan huɗu da dubu ɗari biyu.

Tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ne ya sace kuɗin kuma ya kai ƙasar Burtaniya, inda aka kama shi da laifi.

'Yan majalisar sun ce kuɗin halaliyar jihar Delta ne, tun da daga asusunta aka sace su.

Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilan ƙasar ne ya gabatar da ƙudurin yana cewa kamata ya yi a saka kuɗin a cikin asusun gwamnatin jihar Delta, ba asusun gwamnatin Tarayya ba.

Majalisar wakilan ta amince a turo da kwamatoci zuwa wurin ministar kuɗi da ministan shari'a domin su tattauna da juna a kan ko wani ɓangare ya kamata a bai wa kuɗin.

Sai dai tun farko ministan sharia na Najeriya Abubakar Malami ya ce ba bu wani shiri da ya wajabta maida kuɗin ga gwamnatin jihar Delta.

Amma Hon Abdurrazak Namdas wanda mamba ne a majalisar wakilan ya ce yana da muhimmanci a warware wannan rigimar .

"Yan jihar Delta ne za su fi amfana da wannan kuɗi don gobe idan wani gwamna ya saci kuɗi idan za a dawo da shi Najeriya, toh dan Allah ya koma wannan jiha."

A 2012 ne Burtaniya ta samu tsohon gwamnan da laifin satar kuɗaden tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 13 a gidan yari.

Tsohon gwamnan, ya amsa laifi a gaban kotun London, bisa jerin tuhume- tuhume goma da aka yi masa na salwantar da kuɗaɗen haram, da kuma haɗa baki domin tafka zamba.

Wannan ne karon farko da za a dawo wa Najeriya kuɗaɗen da masu laifi suka sace tun yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a 2016, kamar yadda hukumomin Burtaniya suka bayyana.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi amfani da kuɗaden domin kammala ayyukan da take yi na raya ƙasa.