Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 28Article 451008

BBC Hausa of Friday, 28 May 2021

Source: BBC

Ku San Malamanku tare da Malam Yakubu Musa

Malam Yakubu Musa Malam Yakubu Musa



Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Malam Yakubu Musa, shi ne shugaba na farko na majalisar Shari'ar Musulunci a Najeriya mai suna Supreme Council for Shari'a in Nigeria kuma masanin Shari'a wanda ya yi karatu a wurare daban-daban.

Malamin, wanda ɗan ɗariƙar Tijjaniyya ne a baya, shi ne shugaban ƙungiyar Izala na Jihar Katsina ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

An haifi Yakubu Musa a garin Gagaryaga da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gwaram - ta Jihar Jigawa a yanzu - ranar 1 ga watan Janairun 1950.

Ya yi karatun Alƙur'ani a garuruwan Kano da Jigawa da Katsina da Jos. Yanzu mazaunin Katsina ne, inda ya shafe kusan shekara 40 a garin.

Neman ilimi

Iyayen Malam Yakubu sun kai shi birnin Kano tun yana shekara bakwai da haihuwa domin ya ci gaba da karatun Alƙur'ani a wajen ƙanin mahaifinsa mai suna Malam Mamuda, wanda aka fi sani da Malam Mudi a unguwar Karofin Zage.

Bayan ya fara karatun Iziyya da Risala, sai malam ya koma gida domin taya mahaifinsa aiki.

Ya ci gaba da karatu a hannun Malam Yahaya Tamaji a garin Gwaram wanda ke cikin Jihar Jigawa a yanzu, inda ya karanta litattafai da dama.

Ya koma garin Jos na Jihar Filato a shekarar 1970 domin yin kasuwanci, amma sai ya ɓige da ɗorawa da karatu a hannun malamai guda uku.

Ya shiga makarantar dare mai suna Misbahudden. An zaɓe shi a cikin ɗalibai mafiya hazaƙa kuma aka buɗe musu ɓagaren sakandare, inda suka ci gaba da karatun Ƙur'ani da Nahawu da Tafsiri a wajen wani malami ɗan ƙasar Bangaledash.

A shekarun 1980 malam ya samu tallafin karatu zuwa Masar amma bayan ya yi shawara da jagoran ƙungiyar Izala, Mahmud Abubukar Gumi, da kuma iyalinsa sai ya fasa tafiya.

Daga bisani ya shiga kwalejin Shari'a ta Katsina, inda ya samu difiloma a Shari'a.

'Na gode wa Allah da ya sa na bar ɗarika'

"Gaskiya babu abin da nake murnarsa kamar yadda Allah ya fitar da ni daga ɗariƙa ya sanya ni cikin mabiya Sunnar Annabi," a cewar Malam Yakubu Musa.

Malam ya ce karatun da ya fi masa tasiri a rayuwarsa shi ne Alƙur'ani.

Wannan dalili ne ya sa malamin da ya fi tasiri har wa yau a rayuwarsa shi ne Muslim Khan, ɗan asalin

Sana'a

Shehin malamin ya ce ya yi sana'o'i da yawa da suka haɗa da ƙira, wadda ya koya a Kano.

Bayan ya koma Gwaram, ya yi sana'ar fenti da kuma ƙera akwatuna, har ma ake kiran sa da Malam Yakubu Mai Adaka.

Komawarsa garin Jos ke da wuya, sai ya shiga sana'ar hayar keke. Kazalika, ya yi sana'ar faci da kuma sayar da taya, inda suka dinga sayo su daga wasu jihohi suna sayarwa a matsayin sakanhan.

Iyali

Ya zuwa lokacin wannan hira, Malam Yakubu Musa na da mata uku da 'ya'ya 26 - maza 15 da kuma mata 11.

Kazalika, malam na da jikoki kusan 80.