Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 02Article 450551

BBC Hausa of Sunday, 2 May 2021

Source: BBC

Kotu a Brazil ta tsige gwamnan da ya ce zai riƙa yanka masu laifi

Gwamnan Rio de Janeiro, Wilson Witzel da aka tsige shi akan zargin cin hanci da rashawa Gwamnan Rio de Janeiro, Wilson Witzel da aka tsige shi akan zargin cin hanci da rashawa

Wata kotu ta musamman a Brazil ta tsige gwamnan Rio de Janeiro, Wilson Witzel kan zargin cin hanci da rashawa a sayen kayayyakin kiwon lafiya don kula da masu fama da cutar korona.

Mista Witzel tsohon aboki ne ga Shugaba Jair Bolsonaro kuma an zabe shi yana mai alkawarin "yanka masu laifi," kamar yadda ya fada.

Ya musanta aikata wani laifi, kuma ya ce abokan siyasa na Mista Bolsonaro sun tsananta masa bayan da ya samu sabani da shi.

An dakatar da shi daga mukaminsa na gwamna a watan Agusta, lokacin da aka fara shirin tsige shi.