Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 22Article 449797

BBC Hausa of Monday, 22 March 2021

Source: BBC

Ko Tuchel zai doke Guardiola a FA Cup a daf da karshe?

Za a buga wasan karshe a FA Cup ranar 15 ga watan Mayu a Wembley Za a buga wasan karshe a FA Cup ranar 15 ga watan Mayu a Wembley

Wadda ta lashe kofin kalubalen Ingila karo takwas, Chelsea za ta fafata da Manchester City mai harin lashe kofi hudu a bana a wasan daf da karshe a FA Cup.

Daya wasan kuwa za a yi ne tsakanin Leicester City da Southampton da ake sa ran yin gumurzun ranar 17 da kuma 18 ga watan Afirilu a Wembley.

Chelsea ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta doke Sheffield United da ci 2-0 ranar Lahadi.

Leicester kuwa wadda ba ta taba lashe FA Cup ba duk da kai wa wasan karshe karo hutu ta zo wannan matsayin bayan cin Manchester United 3-1.

Za a buga wasan karshe a FA Cup ranar 15 ga watan Mayu a Wembley.

Watakila magoya baya kimanin 20,000 su kalli wasan karshen, domin daya ne daga karawar da gwamnatin Burtaniya ta amince a yi don gwajin yadda 'yan kallo za su koma ganin wasanni ido da ido.

Yadda aka raba raba jadawalin daf da karshe a FA Cup:

Leicester da Southampton

Chelsea da Manchester City