Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 16Article 450811

BBC Hausa of Sunday, 16 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Zidane, Ancelotti, Pogba, Holgate, Koulibaly, Camavinga

Kociyan Real Madrid Zinedine Zidane Kociyan Real Madrid Zinedine Zidane

Kociyan Real Madrid Zinedine Zidane ya gaya wa 'yan wasan kungiyar zai ajiye aikinsa a karshen kakar da ake ciki. (Jaridar Goal)

Hakan ya sa tuni kungiyar ta fara tunin daukar wanda zai maye gurbinsa, daga cikinsu akwai kociyan Everton Carlo Ancelotti da tsohon kociyan Juventus Massimiliano Allegri. (Jaridar Sunday Mirror)

Manchester United na son dan wasanta na tsakiya Paul Pogba, mai shekara 28, ya ci gaba da zama a kungiyar, ya kulla sabuwar yarjejeniya da ita, amma kuma tana tsoron yawan albashin da wakilin dan wasan na Faransa, Mino Raiola, ke neman a rika ba Pogban. (JaridarSunday Mirror)

Everton ta ce a shirye take ta sayar da dan bayanta Mason Holgate, dan Ingila, mai shekara 24, domin ta samu kudin da za ta ganganda ta sayo dan bayan Napoli Kalidou Koulibaly, dan kasar Senegal, mai shekara 29. (Jaridar Football Insider)

Arsenal na fatan kasa Manchester City wajen daukar Ryan Bertrand, dan Ingila mai shekara 31. Dan bayan zai bar Southampton idan kwantiraginsa ya kare a karshen kakar nan. (Jaridar Mail ta Lahadi)

West Ham ta kasance ta gaba-gaba da za ta yi nasara wajen daukar mai tsaron ragar West Brom Sam Johnstone. Kafin yanzu ana danganta golan dan Ingila mai shekara 28 da shirin tafiya Tottenham. (Jaridar Football Insider)

Kociyan Barcelona da ke shan matsin lamba Ronald Koeman ya gana da shugaban kungiyar Joan Laporta, kuma ya ce za su sake ganawa a karshen kakar nan. (Jaridar Goal)

Eintracht Frankfurt na son nada tsohon dan gaban Real Madrid Raul a matsayin kociyanta a kaka ta gaba.(Jaridar Marca)

Real Madrid na son sayen dan wasan tsakiya na Faransa Eduardo Camavinga daga Rennes, amma kuma Arsenal ma na son matashin dan wasan mai shekara18. (Jaridar Marca)

Kungiyoyin Jamus Bayern Munich da Borussia Dortmund na sa ido a kan matashin dan wasan gaba na Sheffield United, haifaffen Canada, Daniel Jebbison mai shekara 17, na tawagar 'yan kasa da shekara 18 ta Ingila. (90 Min)

Bristol City da Cardiff City da kuma Middlesbrough, kowacce na son daukar dan wasan gaba na Jamhuriyar Ireland James Collins, mai shekara 30, wanda kwantiraginsa da Luton Town zai kare. (Jaridar Mail ta Lahadi)