Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 26Article 450964

BBC Hausa of Wednesday, 26 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Zaha, Martinez, Neves, Coutinho, Willian

Kwararren dan wasan Brazil Philippe Coutinho Kwararren dan wasan Brazil Philippe Coutinho

Tottenham da Everton na son sayen dan wasan gaba na Crystal Palace, dan Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 28, a kan fam miliyan 40. (Jaridar Goal)

Kociyan Paris St-Germain Mauricio Pochettino na matukar tunanin sake komawa tsohuwar kungiyarsa, Tottenham. (Jaridar Sun)

Sai dai kuma tuni kungiyar, ta fara tattaunawa da kociyan Belgium, kuma tsohon mai horad da 'yan wasan Everton da Wigan Roberto Martinez, mai shekara 47, yayin da take ci gaba da neman wanda zai maye gurbin Jose Mourinho. (Sky Sports)

Kwararren dan wasan Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 28, na daga cikin 'yan wasa goma da Barcelona za ta sayar a bazaran nan. (Jaridar Star)

Barcelona da Manchester City na daga cikin kungiyoyin da suke son sayen dan wasan tsakiya na kungiyar Atalanta Robin Gosens, dan Jamus mai shekara 26. (Sport)

Arsenal da Aston Villa za su yi gogayya wajen sayen dan wasan tsakiya na Norwich City Emiliano Buendia, dan Argentina mai shekara 24. (Jaridar Telegraph)

Dan wasan gaba na Arsenal Willian, mai shekara 32, na sha'awar komawa tsohuwar kungiyarsa Chelsea - kasa da wata 12 bayan da dan Brazil din ya kawo karshen zamansa na shekara bakwai a Stamford Bridge. (Sky Sports)

Chelsea za ta iya sayar da dan wasanta na tsakiya, dan Ingila Callum Hudson-Odoi, mai shekara 20, wanda ake ganin Borussia Dortmund za ta iya kasancewa makomarsa. Haka kuma ana ganin kila Dortmund din za ta duba yuwuwar sayen dan wasan gaba na Leeds United Raphinha, dan Brazil mai shekara 24. (Eurosport)

West Ham na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Spartak Moscow, dan kasar Czech Alex Kral, mai shekara 23. (Sky Sports)

Dan bayan Villarreal kuma dan Sifaniya Pau Torres, mai shekara 24, ya ki yarda ya yi magana a kan rahotannin cewa zai koma Manchester United a bazaran nan, kafin wasansu na karshe na Kofin Turai na Europa na ranar Laraba da kungiyar ta gasar Premier. (Jaridar Metro)

Manchester United din kuma ta yarda ta dauki mai tsaron ragar Aston Villa, dan Ingila Tom Heaton, mai shekara 35, ba tare da ta biya wani kudi a kansa ba a wata mai zuwa. (Jaridar Express)

Mai yiwuwa Liverpool ta bayar da aron matashin dan bayanta na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 Rhys Williams, mai shekara 20, a kaka ta gaba duk kuwa da cewa ya samu shiga tawagar 'yan wasan kungiyar na farko a kakar 2020-21. (Jaridar Star)

Dan wasan tsakiya na Arsenal, dan Uruguay Lucas Torreira zai yanke shawara a kan makomarsa bayan wasannin neman zuwa gasar cin Kofin Duniya na wata mai kamawa.Dan wasan mai shekara 25 ya shafe kakar da ta kare a zaman aro a Atletico Madrid. (Jaridar Express)

Watakila kuma Gunners din su sake nuna sha'awarsu ta sayen dan wasan tsakiya na Lyon, dan Faransa Houssem Aouar, mai shekara 22. (Jaridar Mirror)

Wolves a shirye take ta sayar da dan wasan tsakiya dan Portugal Ruben Neves a kan fam miliyan 35, domin samun kudin da za ta kara karfi kan duk wanda zai zo kungiyar bayan tafiyar Nuno Espirito Santo. (Jaridar The Athletic)

Sai dai ba za a tilasta wa Wolves din sayar da Neves mai shekara 24 ba, wanda ya kasance a kungiyar tun 2017, illa dai za ta saurari tayi a kansa idan hakan zai ba ta damar kara karfafa kanta. (Jaridun Express da Star)