Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 17Article 450825

BBC Hausa of Monday, 17 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Tielemans, Willian, Allegri, Raul, Xavi, Alderweireld, Locatelli

Willian, dan kwallon Arsenal Willian, dan kwallon Arsenal

Dan wasan gefe na Brazil Willian zai bar Arsenal a bazaran nan amma kuma har yanzu kungiyar ba ta samu wani tayi ba a kan dan wasan mai shekara 32. (Jaridar Fabrizio Romano daga Mail)

Tsohon kociyan Juventus Massimiliano Allegri ya shiga gaban tsohon dan wasan gaban Real Madrid Raul a matsayin wanda ake sa ran zai maye gurbin Zinedine Zidane a matsayin kociyan kungiyar. (Jaridar Marca)

Barcelona ta fara tattaunawa da tsohon dan wasanta na tsakiya kuma kociyan kungiyar Al Sadd ta Qatar, Xavi domin maye gurbin Ronald Koeman a matsayin kociyan kungiyar. (Jaridar ARA Esports)

Dan wasan baya na Netherlands Sven Botman, wanda ake dangantawa da tafiya Liverpool a watan Janairu, ya ce gasar Premier wata aba ce ta musamman, amma kuma dan wasan mai shekara 21 ya kara da cewa a yanzu yana jin dadinsa a kungiyarsa ta Faransa Lille. (Jaridar Athletic)

Kungiyar Club Bruges na son daukar dan bayan Tottenham Toby Alderweireld, amma kuma dan tawagar ta Belgium mai shekara 32 ba zai yanke shawara ba kan makomarsa har sai ya san wanda zai gaji kociyan wucin-gadi na Tottenham din Ryan Mason. (Voetbal 24, ta Jaridar Express)

Dan wasan tsakiya na Belgium Youri Tielemans zai tattauna kan kwantiraginsa da Leicester City a karshen kakar da ake ciki. Dan wasan mai shekara 24, wanda ya ci wa kungiyar kwallon da ta dauki kofin FA a karawarsu da Chelsea, yana da sauran shekara biyu a kwantiraginsa na yanzu. (Jaridar Mail)

Leeds United da Burnley sun bi sahun Southampton da Watford da kuma Rangers wajen zawarcin dan wasan gaba na gefe na Newcastle United Jacob Murphy, mai shekara 26. (Daga Football Insider)

Crystal Palace na son karbar aron dan wasan baya na Romania, Radu Dragusin, mai shekara 19, daga Juventus. (Jaridar Sun)

Dan wasan tsakiya na Turkiyya Hakan Calhanoglu mai shekara 27, wanda kwantiraginsa da AC Milan zai kare ranar 30 ga watan Yuni, y ace makomarsa ba za ta dogara ga zuwan kungiyar gasar Zakarun Turai ba, saboda haka zai tattauna da kungiyar a karshen kakar nan. (Sky Sport Italia, daga Football Italia)

Darektan Sassuolo Giovanni Carnevali ya ce abu ne da zai iya yuwuwa sosai ma a ce dan wasan tsakiya na Italiya Manuel Locatelli ya zauna a kungiyar ta Serie A zuwa kaka ta gaba, duk da rahotannin da ake bayarwa cewa dan wasan mai shekara 23 zai tafi wasu kungiyoyi. (Sky Sport Italia daga Football Italia)