Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 18Article 450841

BBC Hausa of Tuesday, 18 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Kane, Mendes, Moreno, Trippier, Flick, Bissouma, Sulemana

Harry Kane, dan kwallon Tottenham da kuma tawagar Ingila Harry Kane, dan kwallon Tottenham da kuma tawagar Ingila

Dan wasan gaba na Ingila Harry Kane ya sake gaya wa Tottenham cewa yana son barin kungiyar ta Premier a karshen kakar da ake ciki. Manchester City da Chelsea da kuma Manchester United dukkaninsu sun nuna sha'awarsu ta saukar dan kwallon mai shekara 27. (Sky Sports)

Manchester United na shirin gogayya da abokiyar hamayyarta Manchester City inda ta shirya kashe fam miliyan 52 domin sayen matashin dan bayan Sporting Lisbon Nuno Mendes, dan Portugal mai shekara 18. (Jaridar Mail)

Rahotanni na cewa dan wasan Ingila Kieran Trippier na shirin komawa gasar Premier, inda tuni aka ce Manchester United da Everton na shirin fafatawa domin daukar dan bayan na Atletico Madrid, mai shekara 30. (Athletic)

Brighton & Hove Albion ta fito fili ta gaya wa Liverpool da Arsenal cewa duk wadda take son dan wasanta na tsakiya Yves Bissouma, dan kasar Mali mai sheakara 24 to sai ta biya akalla fam miliyan 40. (Jaridar Sun)

Manchester United ta shiga gaban Ajax a fafutukar da suke yi ta sayen matashin dan wasan gaba na Ghana Kamaldeen Sulemana daga kungiyar FC Nordsjaelland, bayan tattaunawa mai aramashi da suka yi kan cinikin ranar Litinin. (Jaridar Football Insider)

Dan bayan Sifaniya Marcos Alonso, mai shekara 30, da abokin wasansa Emerson Palmieri mai shekara 26, dan kasar Italiya na matsawa domin Chelsea ta bar su, su tafi a karshen kakar nan, domin gwada sa'arsu a gasar Italiya, Serie A. (Jaridar Gazzetta dello Sport)

Dan wasan baya dan kasar Holland Patrick van Aanholt, mai shekara 30, na shirin barin Crystal Palace idan kwantiraginsa ya kare a bazara. (Jaridar Athletic)

Ana sa ran dan wasan gaba na Lyon, dan kasar Holland Memphis Depay, mai shekara 27, zai kammala komarsa Barcelona da aka dade ana sa rai, kafin gasar Zakarun Turai ta bazaran nan, a lokacin bas hi da kwantiragi da wata kungiya. (Jaridar L'Equipe)

Dan wasan tawagar Ivory Coast kuma tsohon dan wasan Arsenal na gaba Gervinho, mai shekara 33, na shirin barin kungiyar Parma, wadda ta fadi daga gasar Serie A ta Italiya, a karshen kwantiraginsa, domin tafiya kungiyar Trabzonspor. (Jaridar Goal ta Turkiyya)

Leeds United da zakarun Scotland Rangers na kokarin saye dan wasan gaba na kungiyar America de Cali, Santiago Moreno, dan kasar Colombia, mai shekara 21. (Jaridar Football Insider)