Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 17Article 450275

BBC Hausa of Saturday, 17 April 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Bellingham, Fofana, Dembele, Alaba, Mbappe, Neymar, Modric, Messi

Raphael Varane, dan kwallon Real Madrid Raphael Varane, dan kwallon Real Madrid

Chelsea na sha'awar sayen matashin dan wasan Ingila na tsakiya Jude Bellingham, mai shekara 17, daga Borussia Dortmund, wadda ta ce farashinsa ya kai fam miliyan 100. (Jaridar Eurosport)

Manchester United na sa ido a kan ci-gaban dan wasan baya na Leicester City Wesley Fofana, dan Faransa mai shekara 20. (Jaridar Foot Mercato ta Faransanci)

Liverpool na son sayen dan wasan gaba na Barcelona Ousmane Dembele, na Faransa mai shekara 23 ,domin maye gurbin Sadio Mane, dan Senegal mai shekara 29. (Jaridar Fichajes ta Sifaniyanci)

Arsenal na sha'awar sayen dan wasan gaba na Inter Milan Martin Satriano kuma Chelsea da Manchester City ma na harin dan wasan na Uruguay mai shekara 20 (Jaridar Mail)

Dan wasan baya na Bayern Munich dan Austria David Alaba, mai shekara 28, ya kulla yarjejeniyar tafiya Real Madrid, bayan yarjejeniyar zamansa a Bayern ta kare a bazaran nan, amma kuma kungiyar tasa ba za ta bayyana labarin ba, sai bayan kakar da ake ciki. (Jaridar Marca)

Mai horad da 'yan wasan Paris St-Germain Mauricio Pochettino na da kwarin guiwa dan wasansa nag aba na Brazil Neymar, mai shekara 29, da kuma Kylian Mbappe, na Faransa mai shekara 22, za su kasance a kungiyar a kaka ta gaba. (Jaridar Cadena SER ta Sifaniyanci)

Real Madrid na son sayar da dan wasanta na gaba dan Wales, Gareth Bale mai shekara 31, wanda yanzu yake zaman aro a tsohuwar kungiyarsa Tottenham, da kuma dan wasanta na baya, dan Faransa Raphael Varane, mai shekara 27, a bazara domin samun kudin sayen Mbappe da kuma dan gaban Borussia Dortmund na kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20. (Jaridar Marca)

Dan wasan tsakiya na Arsenal da Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 25, wanda yanzu yake zaman aro a Atletico Madrid, y ace yana son tafiya Boca Juniors aro. (Jaridar Perfil Bulos, ta ruwaito daga Sun)

Shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce ya gamsu cewa, dan wasansu nag aba na kasar Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, na son ci gaba da zama a kungiyar. (Jaridar Deportes Cuatro, daga Sport)

Dan wasan gaba na Eintracht Frankfurt Andre Silva, wanda Manchester United da Atletico Madrid, ke harin saye ba shi da damar barin kungiyar kafin lokacinsa ya yi, kamar yadda yarjejeniyar sayensa ta nuna. (Goal)

Barcelona ma ta so sayen Silva, amma daga baya ta fasa sayen dan wasan mai shekara 25 dan kasar Portugal. (Jaridar Mundo Deportivo)

Liverpool na tattaunawa sosai a kan kwantiragin Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, wanda hakan ke nufin, dan wasan tsakiyar na Holland zai iya barin Anfield a karshen kakar nan. (Jaridar Liverpool Echo)

Dan wasan baya na RB Leipzig Ibrahima Konate mai shekara 21, ya ce duk da rade-radin da ake yi cewa Liverpool na son sayensa, dan Faransar ya ce shi har yanzu bai ji wata magana daga kungiyar ta Premier ba. (Jaridar Bild ta Jamus)

Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema, mai shekara 33, na dab da kulla yarjejeniyar tsawaita zamansa a kungiyar har zuwa shekara ta 2023. (Jaridar Marca)

Shi kuwa Luka Modric, dan Crotia, mai shekara 35, ya amince da rage masa albashi ya ci gaba da zama a Real Madrid din na karin shekara daya. (Jaridar AS)