Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 16Article 449679

BBC Hausa of Tuesday, 16 March 2021

Source: BBC

Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Ronaldo, Aguero, Haaland, Eriksen

Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo

Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, shi ne "makomar" Juventus, a cewar daraktan kungiyar ta Serie A, Fabio Paratici. (ESPN)

Barcelona na dab da kulla yarjejeniyar daukar dan wasan Manchester City Sergio Aguero amma sayen dan kwallon mai shekara 32 a bazara zai dogara ne da matakin da kungiyar ta Nou Camp za ta iya dauka na rarrashin dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, domin ya ci gaba da zama da su. (AS)

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer zai iya sayar da dan wasan Ingila mai shekara 28 Jesse Lingard, da dan wasan Sifaniya mai shekara 32 Juan Mata, da dan wasan Portugal mai shekara 21 Diogo Dalot da kuma dan kasar Ingila mai shekara 29, Phil Jones, domin ya samu £80m da zai kara a cikin kasafin kudinsa na bazara. (Metro)

Daraktan wasanni na Borussia Dortmund Michael Zorc ya ce kungiyarsa za ta mayar da hankali wajen samun gurbin zuwa gasar Zakarun Turai ta hanyar Bundesliga a yayin da take kokarin rike dan wasan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, ya zuwa "tsawon lokaci mai yiwuwa". (Welt an Sonntag, via Goal)

Manchester City ta tuntubi Sporting Lisbon game da dan wasanta Nuno Mendes a yayin da take son shan gaban Real Madrid a kokarin daukar dan wasan na Portugal mai shekara 18. (AS, via Mail)

Arsenal na son daukar dan wasan Eintracht Frankfurt dan kasar Faransa Evan N'Dicka, mai shekara 21, sannan ta nemi a sanar da ita halin da dan wasan Brighton da Mal mai shekara 24 Yves Bissouma yake ciki. (Express)

Dan wasan Inter Milan Lautaro Martinez, mai shekara 23, yana da kwarin gwiwar sabunta kwangilarsa a kungiyar, duk da abin da dan kasar ta Argentina ya bayyana a matsayin "hali na rashin kudi" da yake fama da shi a kungiyar ta kasar Italiya. (Sky Sports Italia, via Goal)

An ce dan wasan Denmark Christian Eriksen zai bar Inter Milan a watan Janairu sai dai dan wasan mai shekara 29 ya ce yana jin dadin zama a kungiyar da ke buga gasar Serie A. (Sky Sports Italia, via Football Italia)

Chelsea tana son karbar a kalla euro 20m kan dan wasan Italiya Emerson Palmieri, a yayin da Inter Milan da Napoli suke sha'awar dan wasan mai shekara 26. (Calciomercato, via Football Italia)

Mahaifin matashin dan wasan Barcelona Ilaix Moriba ya ce ya hana dansa bin jirgin da zai tafi Manchester yayin da dan wasan mai shekara 18 dan kasar Sifaniya yake dab da komawa Manchester City a 2019. (Sport)