Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 04Article 449480

BBC Hausa of Thursday, 4 March 2021

Source: BBC

Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Haaland, Lamptey, Aarons, Bellerin, Aguero, Arteta

Dan wasan gaba na Borussia Dortmund Erling Braut Haaland Dan wasan gaba na Borussia Dortmund Erling Braut Haaland

Dan wasan gaba na Borussia Dortmund Erling Braut Haaland mai shekara 20 kuma dan kasar Norway ya ce akwai kungiyoyi shida da zai so komawa, amma Liverpool, Manchester United da Manchester City ne kungiyoyin da yafi so a gasar Firimiyar Ingila. (Bild, via Sun)

Dortmund sun ce za su so su ci gaba da rike Haaland har kakar wasa mai shigowa, kamar yadda Sebastian Kehl, daya daga cikin shugabannin kungiyar ya sanar. (London Evening Standard)

Arsenal na duba yiwuwar dauko Tariq Lamptey dan wasan baya na Brighton mai shekara 20 da dan wasan baya Max Aarons na kungiyar Norwich mai shekara 21 domin maye gurbin Hector Ballerin mai shekara 25 da ake sa ran zai koma Paris St-Germain. (Sun)

Chelsea za ta rika samun wani kaso na kudin da za a biya Brighton kan Lamptey bayan yarjejeniyar cinikinsa da ta shiga ciki da ya raba dan wasan bayan daga Stamford Bridge zuwa kungiyar Seagulls din a Janairun 2020. (Express)

    Juventus ta mallaki Weston McKennie daga Shalke 04 2021 Afcon qualifier: Super Eagles za ta kara da Lesotho a Legas
Dan takararar mukamin shugaban Barcelona Joan Laporta ya ware Sergio Aguero, dan wasan gaba na Manchester City a matsayin wanda zai saya a karshen wannan kakar wasan. (Mail)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce ya mayar da hankalinsa kan kai Arsenal gaci ayyin da ake hasashen komawarsa Barcelona - amma ya yarda cewa har zuwa wannan lokacin ba a tuntube shi ba kan sabunta kwantiraginsa a Emirates. (ESPN)

Arteta ya kuma ce za a fara tattaunawa kan tsawaita kwantiragin Alexandre Lacazette, dan wasan gaba na Faransa mai shekara 29 wanda wa'adin wasan da yake bugawa zai kare a 2023. (Mail)

Tsohon dan wasan gefe ba Ingila Ashley Young mai shekara 35 na fatan lashe kofinsa na farko da Inter Milan kafin ya koma kungiyarsa a farko Watford a karshen wannan kakan wasan na bana. (Mirror)

Jurgen Klopp ya yarda cewa Liverpool za ta fuskanci cikas wajen dauko sabbin 'yan wasa idan kungiyar ta kasa shiga cikin kungiyoyi hudu na farko da za su buga gasar Zakarun Turai. (Goal)