Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 10Article 449584

BBC Hausa of Wednesday, 10 March 2021

Source: BBC

Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar De Gea, Oblak, Torres, Mahrez

Mai tsaron raga David de Gea Mai tsaron raga David de Gea

Manchester United za ta saurari tayin sayen mai tsaron raga David de Gea mai shekara 30 a kakar wasan nan inda this kocin ƙungiyar Ole Gunnar Solskjaer yake a shirye ya mayar da Dean Henderson na ɗaya. (90min via Mail)

Rahotanni sun ce Arsenal a shirye take ta yi amfani da dambarwar da ke faruwa a Inter Milan wajen gabatar da buƙatarta ta neman ɗan wasan baya na Morocco mai shekara 22 Achraf Hakimi. (Mirror)

Manchester United da Manchester City sun nuna sha'awarsu ta sayen ɗan wasan Villarreal Pau Torres mai shekara 24. (Manchester Evening News)

    PSG ta yi magana kan makomar Mbappe da Neymar, Man Utd na son Rice 'Yan Real Madrid da za su fafata da Sociedad ran Litinin
Crystal Palace na yunƙurin neman ɗan wasan tsakiya na Sheffield United John Lundstram mai shekara 27 da ɗan wasan tsakiya na Chelsea Conor Gallagher mai shekara 21 yayin da suke shirin yin mahimman sauye-sauye a kakar wasan nan. (Express)

Ɗan wasan Schalke ɗan Spaniya Omar Mascarell mai shekara 28 ya zama mai taka ledae da Wolves ke nema a kakar wasa ta bana. (Caught Offside)

Kocin Manchester City Pep Guardiola na fatan ya gamsar da ɗan wasan Argentina Sergio Aguero mai shekara 32 ya ci gaba da zama a ƙungiyar. (Star)

Real Madrid na bayyana sha'awar sayen ɗan wasan Manchester City da Algeria Riyad Mahrez ɗan shekara 30. (FootMercato - in French)

Ɗan wasan Celtic da Scotland Jack Hendry mai shekara 25 da rahotanni suka ce Aston Villa na zawarcinsa, tsadarsa za ta iya kaiwa £10m a kakar wasa ta bana. (Birmingham Mail)

Barcelona ta cimma yarjejeniya da Bayern Munich kan ɗan wasan Austria David Alaba mai shekara 28. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Inter Milan ta tuntuɓi wakilin ɗan wasan Real Betis Aissa Mandi mai shekara 29, wanda ake raɗe-raɗin Liverpool na zawarcinsa a watan Janairu. (Calciomercato - in Italian)