Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 06 03Article 451135

BBC Hausa of Thursday, 3 June 2021

Source: BBC

Kasuwar ƴan ƙwallo: Mbappe, Lukaku, Wijnaldum, Trippier, Wood, Firpo

Kyliam Mbappe, dan wasan PSG da tawaggar Faransa Kyliam Mbappe, dan wasan PSG da tawaggar Faransa

Real Madrid za ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan gaba Kylian Mbappe, mai shekara 22, daga Paris St-Germain, da ke shirin ɗauko ɗan wasan gaba a Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, daga Juventus, yayin da ɗan wasan Argentina Mauro Icardi, mai shekaru 28, zai koma PSG daga Juve. (La Gazzetta dello Sport, via Mail)

Real Madrid ta tuntuɓi Jose Mourinho a makon da ya gabata, kafin su sanar da sabon kocinsu Carlo Ancelotti, duk da cewa tsohon kocin Real ɗin da Tottenham ya amince ya koma Roma a watan da ya gabata. (Telegraph - subscription required)

Burin Chelsea na dawo da Romelu Lukaku ƙungiyar ya fuskanci tasgaro bayan ɗan wasan mai shekara 28 dan asalin Belgium ya sanar da cewa zai ci gaba da zama a Inter Milan. (Football Italia)

Barcelona na tattaunawa da ɗan wasan gaban Dutch, Memphis Depay, mai shekara 27, kan komawa Lyon, yayin da mai buga wa Dutch tsakiya Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, zai koma Liverpool ba tare da biyan sisi ba. (Fabrizio Romano, Twitter)

Manchester United ta sake farfaɗo da ƙudirinta na cimma yarjejeniya da ɗan wasan Ingila Kieran Trippier, mai shekara 30, daga Atletico Madrid. (Manchester Evening News)

Aston Villa na cikin jeren manyan ƙungiyoyin firimiyar Ingila 12 da ke tsara farautar ɗauko ɗan wasan New Zealand, Chris Wood, kuma Burnley za ta buƙaci aƙalla £30m kan ɗan wasan mai shekara 29. (Football Insider)

West Ham da New York City sun miƙa tayinsu ga ɗan wasan Faransa Olivier Giroud, wanda ke shirin yin adabo da Chelsea.(Calciomercato - in Italian)

Sabon kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce ɗan wasan Wales da ke buga gaba Gareth Bale, da ɗan wasan Belgium, Eden Hazard, na iya samun makoma nan gaba a ƙungiyar. (Guardian)

Dan wasan Borussia Monchengladbach ta Jamus da ke buga tsakiya Florian Neuhaus, da ake alakantawa da Liverpool, ya musanta cimma daidaituwa da Bayern Munich. (Tageszeitung - in German)

Arsenal, Manchester United da Tottenham sun nuna zawarcinsu a kan ɗan wasan Lille na Turkiyya Zeki Celik, mai shekara 24. (Standard)

West Ham da Southampton na fafatawar sayen ɗan wasan Barcelona Junior Firpo, mai shekara 24. (Sport - via The Boot Room)

West Ham ta shiga matakin kololuwa a tattaunawar sayen ɗan wasan Jamhuriyar Czech Alex Kral, 23, daga Spartak Moscow a kan sama da £20m. (Football Insider)

Ɗan wasan Argentina Sergio Aguero, mai shekaru 33, ya yi watsi da tayin Juventus domin komawa Barcelona a kan kyauta daga Manchester City. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Sevilla ta nuna sha'awarta kan ɗan wasan Chile mai buga gaba Alexis Sanchez, daga Inter Milan. (Sport - in Spanish)

Leeds United ta nuna kwadayinta kan ɗan wasan Huesca ta Spaniya Javi Galan, wanda ake neman £3.5m a kansa. (Football Insider)

West Brom ta shirya neman wanda zai maye gurbin kocinta bayan tattaunawa mai zurfi da tsohon kocin Sheffield United Chris Wilder, ɗan shekara 53. (Football Insider)