Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 06Article 450641

BBC Hausa of Thursday, 6 May 2021

Source: BBC

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Konate da Salah da Conte da Lamela da Mata, Williams da Onuachu

Ibrahim Konate, dan wasan baya na RB Leipzig Ibrahim Konate, dan wasan baya na RB Leipzig

Liverpool ta amince da yarjejeniyar da RB Leipzig ta gabatar kan saye ɗan wasan baya Ibrahim Konate mai shekara 21, wanda zai koma taka leda a kungiyar na tsawon shekara biyar.(TalkSport)

West Ham ta shiga jeren kungiyoyin irin Chelsea da ke farautar ɗan wasan Brentford mai shekara 25 Ivan Toney, wanda aka neman £35m a kan sa. (Sun)

Ɗan wasan gaba na Masar Mohamed Salah na son barin Liverpool kuma Paris St-Germain na shirin mika tayinta a kan Sala mai shekara 28 idan Kylain Mbappe, mai shekara 22 ya yi adabo da ita a wannan kakar. (Le Parisien - in French)

Ita kuma PSG na son ƙarawa bayanta ƙarfi don haka yanzu tana harin ɗan wasan Ivory Coast da ke taka leda a Tottenham Serge Aurier. (RMC Sport - in French)

Kungiyoyin firimiya irinsu Norwich City da Southampton da West Ham na fafatawar neman aron ɗan wasan Manchester United da ke buga baya ajin ƴan kasa da shekaru 21 a Ingila Brandon Williams, ɗan shekara 20, a wannan kakar. (Sun)

Tottenham ta tattauna da kocin Inter Milan Antonio Conte a kan komawa gareta. Tattaunawar da kungiyar ta shiga da tsohon kocin Chelsea mai shekara 51 na zuwa ne bayan ya jagoranci Inter zuwa nasara farko a league cikin shekara 11.(Corriere dello Sport, via Express)

Jose Mourinho zai iya tambayar kyeptin ɗin Roma Daniele De Rossi, mai shekara 37, ya zama mataimakinsa idan ya koma jagorantar kulob din. (Calciomercato - in Italian)

Tsohon kocin Spurs Mourinho na iya kokarin ganin dan wasan tsakiyar Tottenham Erik Lamela, mai shekara 29, da Lucas Moura na Brazilian su koma Roma. (Football.London)

West Ham da Crystal Palace sun kwaɗaitu da ɗan wasan RB Leipzig asalin Koriya ta kudu, Hwang Hee-chan, mai shekara 25. (Telegraph)

Yanayin lafiyar ɗan wasan gaban Brazil Wesley, mai shekara 24, wanda ya samu rauni, zai yanke hukunci kan bukatar Aston Villa na nemo wanda zai maye gurbinsa. (Express & Star)

Wolves na da ƙwarin-gwiwar dauko Carlos Vinicius daga Benfica, yayinda Tottenham ba lallai ta tabbatar da zaman aron da yake yi mata ba.(Football Insider)

Dan Najeriya da ke taka leda a Genk Paul Onuachu, mai shekara 26, ya zaku ta koma Arsenal. (Voetbal Belgie - in Dutch)

Benfica da RB Leipzig na zawarcin ɗan wasan Leicester City Sidnei Tavares, sai dai kungiyar na son bijiro da sabon kwantiragi da zai tabbatar da ci gaba da zamansa tare da ita. (Football Insider)

Leeds United ta bada mamaki a salon cimma yarjejeniya da ɗan wasan Turkiyya Ozan Tufan daga Fenerbahce, wanda aka yi tunanin Sifaniya zai koma. (Fotomac - in Turkish)

Julian Nagelsmann na son mai buga wa Inter Milan baya Achraf Hakimi, ɗan shekara 22, ya koma Bayern Munich a kaka mai zuwa. A baya anyi tunanin burin Hakimi shi ne koma wa Arsenal. (Express)

Lazio na duba yiwuwar kulla yarjejeniyar shekara biyu da ɗan wasan Manchester United da ke buga tsakiya Juan Mata mai shekara 33. (Il Tempo - in Italian)

Atletico Madrid ta zagu ta dauko ɗan wasan CA Colon da Argentine Facundo Farias, ɗan shekara 18. (AS - in Spanish)