Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 05Article 450616

BBC Hausa of Wednesday, 5 May 2021

Source: BBC

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Johnstone da Sterling da Bale da Sancho da Kante da Depay

Sam Johnstone, mai tsaron ragar West Brom Sam Johnstone, mai tsaron ragar West Brom

Manchester United ta bi sahun abokan hamayarta na firimiya Tottenham da West Ham wajen neman daidaitawa da mai tsaron ragar West Brom Sam Johnstone, ɗan shekara 28, yayinda David de Gea ɗan Sifaniya ke shirin adabo da ita a wannan kakar. (ESPN)

United na iya kuma sauyawa ta koma farautar mai tsaron ragar Aston Villa Tom Heaton, ɗan shekara 35, saboda watakil Johnstone ya zaɓi koma wa West Ham. (Star)

West Brom za ta buƙaci £20m kan Johnstone idan suka koma kasan teburi a Championship. (Telegraph)

Tsohon ɗan wasan Ingila mai tsaron baya Sol Campbell na cikin jeren mutanen da suka nemi maye gurbin Aidy Boothroyd a matsayin kocin Ingland ajin kasa da shekaru 21. Campbell, mai shekara 46, ba shi aiki a yanzu tun bayan barin sa Southend United a Yuni 2020. (Sun)

Real Madrid ta zura idonta kan ɗan wasan Manchester City da kuma ke buga wa Ingila Raheem Sterling, mai shekara 26, wanda ke iya barin Etihad kan £75m. (Football Insider)

Kocin Everton Carlo Ancelotti na son dauko ɗan wasan gaba a Real Madid da Wales Gareth Bale, mai shekara 31 wanda ke zaman aro a Tottenham a kakar bana, zuwa kungiyar a kaka mai zuwa. (El Chiringuito, via Sport Witness)

Chelsea na iya shiga gasa da Manchester United da Liverpool kan dauko Jadon Sancho bayan Borussia Dortmund ta rage kuɗin da take nema kan ɗan wasan mai shekara 21. (Bild, via Football London)

Kunguiyar ta Bundesliga za ta nemi kusan £85m kan Sancho wannan kakar, kuɗin da ya haura tayin Manchester United. (Eurosport)

Shugaban kulob din Dortmund Michael Zorc ya ce akwai yarjejeniyar da aka cimma da Sancho na sakinsa a wannan kakar. (ARD, via Metro)

Leeds United ta nuna kwadayinta kan ɗan wasan Club Bruges' mai shekara 21, Noa Lang. (Telegraph)

Ɗan wasan bayan nan mai shekara 34 David Luiz ya shiga watannin biyun karshe kafin cikar wa'adin yarjejeniyarsa da Arsenal, wakilinsa sun soma binciken inda zai koma kuma tuni sun mika tayinsa wani kulob a Amurka. (CBS Sports)

Kungiyar mata ta Manchester City na farautar dauko yar wasar Bordeaux mai shekara 24 asalin Jamaica, Khadija Shaw, wacce kuma ake alakantawa da kokarin komawa Amurka. (L'Equipe - in French)

Kungiyoyi da dama sun kwadaitu da dan wasan tsakiya a Norwich City mai shekara Emi Buendia, kungiyoyi irinsu Leeds United ta shiga sahun Arsenal, Aston Villa, Crystal Palace da West Ham, da kuma Atletico Madrid, Sevilla da Villarreal masu farautarsa. (Footmercato - in French)

Dan wasa Anwar El Ghazi, zai ci gaba da zama a Aston Villa a kaka mai zuwa bayan kocinsa Dean Smith ya tabbatar da sakinsa a kasuwar musaya. (Football Insider)

Tsohon shugaban Inter Milan Massimo Moratti ya karfafa gwiwar Nerazzurri kan saye dan wasan Chelsea da Faransa N'Golo Kante, mai shekara 30. (Sky Sport Italia - in Italian)

Borussia Dortmund na burin dauko dan wasan tsakiya Alex Oxlade-Chamberlain daga Liverpool a wannan kakar. (Fichajes - in Spanish)

Barcelona ta tuntubi wakilan ɗan wasan Flamengo Gerson yayinda suke duba yiwuwar sayan dan wasan na Brazil.. (ESPN - in Portuguese)

Dan wasan Lyon da Dutch Memphis Depay, mai shekara 27, na zagu ya cimma yarjejeniya da Barcelona da tuni ta soma farautarsa. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Massimiliano Allegri mai shekara 53 ya bayyana burinsa na koma wa fanin kwallo yayinda ake alakanta shi da Juventus, kuma ana ganin yana iya tafiya Real Madrid.(Tuttosport - in Italian)

Roma da Inter Milan na fafatawa kan dan wasan Uruguay mai shekara 25 Nahitan Nandez. (Calciomercato - in Italian)

Bayern Munich ta yi gaba a cinikin saye ɗan wasan Aston Villa matashi mai shekara 17 Carney Chukwuemeka. (Football Insider)