Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 02 25Article 449440

BBC Hausa of Thursday, 25 February 2021

Source: BBC

Kano Pillars ta hau kan teburin Firimiyar Najeriya

Kano Pillars ta hau kan teburin Firimiyar Najeriya Kano Pillars ta hau kan teburin Firimiyar Najeriya

Kano Pillars ta yi nasarar doke Sunshine Stars da ci 1-0 a wasan mako na 12 a gasar Firimiyar Najeriya da suka fafata ranar Laraba.

Pillars wadda ke buga wasanninta a Kaduna ta ci kwallon ta hannun Nwagua Nyima a bugun tazara a minti na 10 da fara tamaula.

    An nada sabon shugaban Kano Pillars Pillars na fatan daukar Firimiyar Najeriya
Da wannan sakamakon Pillars ta hau kan teburi da maki 23, bayan wasa 12 ta ci fafatawa bakwai da canjaras biyu aka doke ta wasa uku a kakar bana.

Kwara United ce ke mataki na biyu da maki 22, sai Enyimba International ta uku, wadda ta tashi 1-1 da Akwa United a wasan na ranar Laraba.

Sakamakon wasannin mako na 12 da aka buga ranar Laraba:

    Plateau United 3 - 0 Jigawa Golden Stars Nasarawa United 3 - 0 Ifeanyi Ubah Warri Wolves 1 - 0 Rivers United Kada City 1 - 1 Abia Warriors
Wasannin mako na 12 da za a buga ranar Alhamis:

    Katsina United da Mountain Of Fire Adamawa United da Lobi Stars Heartland da Dakkada