Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 25Article 450946

BBC Hausa of Tuesday, 25 May 2021

Source: BBC

Kama dan hamayya: Gwamnatin Belarus ta tsokano Turai da Amurka

Shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von de Leyen Shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von de Leyen

Shugabannin Tarayyar Turai za su gana Litinin din nan domin tattauna yadda za su mayar da martini kan yadda aka tilasta wa jirgin saman da ke dauke da wani dan jarida kuma dan hamayya na Belarus sauka a babban birnin kasar, Minsk.

Shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von de Leyen ta ce za a dauki mataki a kan wadanda ke da hannu a lamarin wanda suka kira fashi.

Wasu manyan jami'an Turan ma sun yi kira ne da a hana jiragen sama zuwa da kuma bi ta kasar ta Belarus.

Haka ita ma Amurka na nazari kan hukuncin da za ta yi a kai.

Hukumomin Belarus sun tilasta wa jirgin saman wanda ya taso daga Athens zai je Lithuania, ya sauka a Minsk inda suka yi karyar cewa an dana bam a jirgin, bayan sun tashi wani jirgin yaki da ya karkatar da shi zuwa babban birnin.

Saukar jirgin na Ryanair a Minsk ke da wuya sai hukumomin suka damke dan jarida kuma dan hamayya Roman Protasevich, mai shekara 26.

Wasu manyan jami'an Turan ma sun yi kira ne da a hana jiragen sama zuwa da kuma bi ta kasar ta Belarus.

Shugabannin Tarayyar Turan za su yi nazari a kan irin tsattauran matakin da za su dauka kan wannan laifi da ya harzuka shugabannin tarayyyar da ma Amurka,

Kan yadda za a ce an tilasta wa wani jirgin sama da ke tafiya tsakanin manyan biranen kasashe biyu na Tarayyar, da aka tilasta masa sauka a wata kasa ta uku da bayyi shirin zuwa ba, kawai domin a kama wani mai hamayya da gwamnatin kasar.

Wannnan shi ne abin da shugabannin Turan za su yi nazari a kai idan suka hadu a Brussels.

Kama Roman Protasevich ya harzuka manyan kasashe da hukumomin duniya to amma, akwai wani mataki na zahiri da zai biyo bayan hakan daga wadanda abin ya harzuka?

Wasu shugabanni da suka hada da Firaministan Poland tuni suka fara kira da a sanya wa gwamnatin Shugaban Lukashenko da suka kira ta kama-karya sabbin takunkumi.

Shugabannin kwamitocin harkokin kasashen waje, daga Birtaniya da Amurka da kuma Tarayyar Turai, sun yi kira da a hana bin jiragen sama ta kasar da ma zuwa Belarus din gaba daya a kana bin da suka kira fashi.

Wasu ma sun bayar da shawarar duba yuwuwar hana manyan motoci daga Belarus din shiga Tarayyar Turai.

Lanmarin ya nuna irin shirin da Shugaba Lukashenko ya yin a danne 'yan hamayya bayan zabensa da ke cike da takaddama a shekarar da ta wuce.

Yanzu ya rage da aga irin matakin da kungiyar kasashen Turai da Amurka za su dauka na ladabtar a shi a kan wannan keta haddi