Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 14Article 449636

BBC Hausa of Sunday, 14 March 2021

Source: BBC

Juyin mulkin Myanmar: Amurka za ta tsugunar da 'yan ƙasar

Shugaban Amurka Joe Biden Shugaban Amurka Joe Biden

Gwamnatin Biden ta ce za ta ba da taimako na ba da mafaka wucin gadi da kuma izinin aiki ga 'yan kasar Myanmar da tuni suka a kasar kuma ke fargabar komawa gida bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan jiya.

Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta ce matsayin na kariya na ɗan lokaci - wanda zai ɗauki watanni goma sha takwas - ya kuma shafi waɗanda ba yan kasar ba da ke yawan zama a Myanmar.

Ya ambaci amfani da mummunar tashin hankali kan fararen hula, da tabarbarewar yanayin agaji da tattalin arziki a kasar da ke kudu maso gabashin Asiya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce shugabannin mulkin sojan Myanmar sun kashe akalla mutane saba'in tare da tsare dubbai a kokarinsu na murkushe masu adawa da juyin mulkin.

Sojojin sun sauya ministoci da mataimakansu da suka haɗa da na kuɗi da na lafiya da na harkokin cikin gida da ƙasashen waje.

Sun kuma toshe kafar Facebook, wacce ake yawan amfani da ita a faɗin ƙsar, da Tuwita da Instagram.

Amma hakan bai yi nasarar hana zanga-zangar da ake yi a ƙasar tun ranar Asabar da Lahadi ba - wacce ita ce mafi girma da ƙasar ta gani tun shekarar 2007, lokacin da dubbai suka nuna adawa da mulkin soji.

Yadda Aung San Suu Kyi ta hau mulki

Aung San Suu Kyi ta kwashe kusan shekara 15 a tsare tsakanin 1989 zuwa 2010.

A 1991, an ba ta lambar yabo ta Nobel Prize yayin da take tsare a gida kuma an yabe ta a matsayin "mai jajircewa duk da rashin ƙarfin ikonta".

Gwamnatin Obama ta cire takunkumin da ke kan Myanmar bayan da suka koma Dimokuraɗiyya

Gwagwarmayarta ta kawo dimokuraɗiyya mulkin soja na wancan lokaci a Myanmar ya sa ta zama wata alama ta son zaman lafiya duk da zaluncin da ke gudana a ƙasar.

A watan Nuwambar 2015 ne ta jagoranci jam'iyyar NKD ta yi nasara a zaɓen dimokuraɗiyya na farko cikin shekara 25.

Kundin tsarin mulkin Myanmar ya haramta mata zama shugaba saboda tana da ƴaƴa da ba ƴan ƙasar ba.

An hamɓarar da shugabar Myanmar da ta goyi bayan yi wa Musulmai kisan kiyashi

Mutumin da ya maka Aung San Suu Kyi gaban kotun duniya

Amma duk da haka ana yi wa Suu Kyi, mai shekara 75 a yanzu kallon shugabar ƙasar mai cikakken iko.

A hukumance ana kiranta 'state counsellor" wato mai bai wa gwamnati shawara. Shugaban ƙasar, Win Myint, na hannun damanta ne.