Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 02Article 449444

BBC Hausa of Tuesday, 2 March 2021

Source: BBC

Ibrahimovic ba zai buga wasa da United a Europa League ba

hh hh

Dan kwallon AC Milan, Zlatan Ibrahimovic zai yi jinyar mako uku, sakamakon raunin da ya yi ranar Lahadi.

Hakan na nufin ba zai buga gasar Zakarun Turai ta Europa League ba, domin fuskantar tsohuwar kungiyarsa Manchester United.

    Ibrahimovic zai bar Man Utd AC Milan ta dauki Ibrahimovic
AC Milan da Manchester United za su kara gida da waje a wasan zagaye na uku a Europa League ranar 11 da watan Maris karawar farko da 18 ga watan Maris wasa na biyu.

Dan wasan mai shekara 39 ya ci wa Manchester United kwallo 29 a wasa 53 da ya yi mata.

Dan kwallon ya yi rauni ne ranar Lahadi a gasar Serie A da AC Milan ta je ta doke Roma da ci 2-1 da hakan ya sa Milan ta ci gaba da zama ta biyu a teburi.

Dan kasar Sweden ya ci kwallo 16 a wasa 21 da ya buga a kakar bana.

Inter Milan ce ta daya a kan teburin Serie A da tazarar maki hudu tsakaninta da AC Milan ta biyu.