Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 26Article 450441

BBC Hausa of Monday, 26 April 2021

Source: BBC

Henry da Bergkamp da Vieira za su sayi Arsenal

Tsoffin fitattun 'yan wasan Arsenal Thierry Henry da Dennis Bergkamp da kuma Patrick Vieira Tsoffin fitattun 'yan wasan Arsenal Thierry Henry da Dennis Bergkamp da kuma Patrick Vieira

Tsoffin fitattun 'yan wasan Arsenal Thierry Henry da Dennis Bergkamp da kuma Patrick Vieira za su sayi kungiyar.

Hakan ya sa sun bi sahun attajiri dan kasuwa Daniel Ek wanda ya kirkiri manhaja Spotify, wanda tuni ya bayyana aniyarsa ta sayen Gunners.

Mai kungiyar Stan Kroenke bai da niyyar sayar da Arsenal, sai dai sama da magoya baya 1,000 sun yi zanga-zanga a filin Emirates ranar Juma'a inda suka bukaci shungaban da ya yi murabus.

Ranar Lahadi da ta gabata Arsenal ta sanar cewar tana daga cikin kungiyoyi 12 da suka shirya gudanar da sabuwar gasar European Super League.

Sauran kungiyoyin da suka amince za su yi wa gasar zakarun Turai kishiya daga Ingila sun hada da Liverpool da Chelsea da Manchester City da Manchester United da kuma Tottenham.

Sauran da suke cikin tafiyar sun hada da Real Madrid da Barcelona da Atletico Madrid da Juventus da Inter Milan da kuma AC Milan.

Daba baya Inter da Milan da kuma Atletico dukkansu suka janye daga shiga sabuwar gasar da ta ci karo da suka tun daga Fifa da Uefa da gwamnatin Burtaniya da masu ruwa da tsaki.

Sai dai awa 24 tsakani dukkan kungiyoyin Premier League shida suka janye daga shirin suka kuma nemi afuwa a wajen magoya baya.

Ranar Juma'a attajiri dan kasar Sweden Ek, mai shekara 38 wanda yake da kudi da ya kai dalar Amurka biliyan 4.7 ya sanar a kafar sada zumuntarsa a Twitter.

''Tun lokacin da nake dan karami, nake ta goyon bayan Arsenal, idan kuma Kronke zai sayar da kungiyar a shirye nake na saya.''

Arsenal tana ta 10 a teburin Premier League da maki 46, za ta buga wasan daf da karshe na farko a Europa League da Villareal a Spaniya.