Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 23Article 450372

BBC Hausa of Friday, 23 April 2021

Source: BBC

Gerd: Sudan ta gargadi Ethiopia kan Kogin Nilu

Sakamakon Gerd, takaddamar difilomasiyya ta kara zafafa tsakanin Sudan, Habasha da Masar Sakamakon Gerd, takaddamar difilomasiyya ta kara zafafa tsakanin Sudan, Habasha da Masar

Sudan ta shafe shekaru goma tana takaddama da kasashen Ethiopia da Masar a kan madatsar ruwan da kasar Ethiopia ke ginawa a kan Kogin Nilu, kuma a cikin watannin baya-bayan nan rikicin ya kai wani matakai, yayin da Zeinab Mohammed Salih ke bayar da rahoto daga birnin Khartoum.

Yayin da ake magana a kan madatsar ruwan ta kasar Habasha da ake kira "Grand Ethiopian Renaissance Dam (Gerd)", kalaman da kasar Sudan ke yi sun tashi daga kawaici sun koma zargi da kuma nuna bacin rai a fili.

Wannan sauyi, a bangarori da dama na nuni da tasiri da karfin fada-a-jin soji a gwamnatin rikon kwaryar da ya kamata a ce ta bayar da dama ga tsarin dimokaradiyya tun bayan da aka hambare gwamnatin shugaban kasar da ya yi dogon zamani Omar al-Bashir.

Takaddamar difilomasiyya ta kara zafafa a yayin da lokacin damuna a kasar Ethiopia ke karatowa kuma tafkin da ke bayan madatsar ruwan zai kara cika ya batse a cikin shekara ta biyu ba tare da wata yarjejeniya kan yadda ya kamata a yi ba.

Duka kasashen Ethiopia da Masar sun yi magana game da aikin da kuma tsarin yadda da za a bi domin yin sulhu.

Ethiopia ta ce madatsar ruwan ta Gerd na da matukar muhimmanci ga ci gabanta saboda za ta samar da karfin wutar lantarki ga kashi 60 bisa 100 na al'ummar kasar.

Kasar Masar ta ce hakan na haifar da barazana ga gudanar ruwan Kogin Nilu da ke taimaka wa rayuwar al'umma a can.

Kasar Sudan, wacce ke kan kogin tsakanin kasashen biyu, yanzu ta dauki matakin yin zafafan gargade-gargade da kan ta.

Mai bayar da shawara ga majalisar lura da al'amuran mulkin kasar Sudan, Laftanal Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya yi magana a kan takaddama game da ruwan kogin "cewa zai iya zama mai muni fiye da yadda ake tunani" muddin kasashen waje ba su taimaka ba wajen warware matsalar.

Sauyi game da karfin iko

Waiwaye cikin watanni 14 da suka gabata da kuma surutai daban-daban na fitowa daga babban birnin kasar, Khartoum.

A watan Fabrairun shekarar 2020, Ministan Albarkatun Ruwa na kasar Yasir Abbas ya yi magana kan yadda madatsar ruwan, mai samar da karfin wutar lantarki mafi girma a Afirka, za ta amfani kasar Sudan.

Yayin da aka san da wasu kananan matsalolin da za a warware, ya ce madatsar ruwan ta Gerd za ta kara wa gudanawar ruwan Kogin Nilun karfi kana zai iya haifar da karin yanayin kakar noma na uku.

Madatsar ruwan kuma ka iya nufin cewa za a samu karuwa da kuma dorewar karfin wutar lantarki a kasar Masar, wacce a baya bayan nan ta fuskanci matsanancin daukewar wutar lantarki har na tsawon sa'oi 12 a rana.

Amma a farkon wannan watan ne bayan tattaunawar kasashen Masar da Ethiopia da Sudan wacce Kungiyar Hadin kan Afirka ta shirya a birnin Kinshasa, Mista Abbas ya shaida wa manema labarai cewa muddin Ethiopia ta cika madatsar ruwan ba tare da warware matsalolin da ke kasa ba, lamarin zai haifar da barazana ga tsaon kasa.

Sudan na bukatar Ethiopia ta rattaba hannu kan yarjejeniya a hukumance a maimakon gindaya wasu dokoki kan adadin ruwan da aka datse ko kuma jadawalin kan cika tafkin.

Ta kuma bukaci a fayyace mata kan yadda za a shawo kan matsalar takaddamar a nan gaba.

Mista Abbas ya kuma shaida wa BBC cewa kasar Ethiopia na bijiro da wasu bukatu game da amfani da ruwan waje aikin noma a yunkurinta na haifar da rudani a batun zaman sasantawar.

"Ba tare da yarjejeniya ba, madatsar ruwan ta Gerd wata babbar barazana ce ga mutanen da ke kwari... duka muhallin da kuma hanyoyin samun kudin shiga na mutane," in ji shi.

Ya kara da cewa Sudan za ta fi fuskantar matsaloli fiye da Masar, idan madatsar ruwan ta rage yawan ruwan da zai rika kawaranya ta cikin Sudan, saboda kasar Masar na da babban tafki da ke bayan madatsar ruwan ta Aswan.

'Nuna wa kasar Ethiopia yatsa'

An dade da sanin wannan. Abin da ya sauye shi ne batun ko wane ne ke da karfin iko tsakanin sojoji da fararen hula a gwamnatin rikon kwarya bayan shugabancin al-Bashir.

Yanzu duk wata barazana ga harkokin tsaron kasa sun wuce sauran batutuwa. Har ila yau, zazzafar damuwar tsakanin kasashen Sudan da Ethiopia game da takaddamar kan iyaka da aka fi sani da al-Fashaga ta hana wa Sudan yin wani sassauci ga kasar Ethiopia.

Ba a shata takamaiman kan iyakar da ke tsakanin kasashen biyu ba kuma duk da yarejeniyar da aka yi a lokacin turawan mulkin mallaka da ke nuna cewa madatsar ruwan al-Fashaga bangare kasar Sudan ne, 'yan kasar Ethiopia suna biyan haraji ga mahukuntan kasar ta Ethiopia.

A shekarar 2008, an cimma wata yarjejeniyar amincewa wacce kasar ta Ethiopia ta yarda cewa a bangare kasar Sudan din take, amma kuma 'yan kasar ta Ethiopian suka ci gaba da zama a can.

Amma kuma Sudan ta yi amfani da damar da ta samu daga Ethiopia wacce a bara ne rikicin yankin Tigray ya dabaibaye ta kuma ta tura dakarunta zuwa yankin na al-Fashaga.

Gwamnati ta kaddamar da babban gangami na samun amincewar mutane su goyi bayan matakin soji a kan yankin.

Wannan ya hada da daukar mutane masu karfin fada-a-ji zuwa kan iyakar da kuma shahararrun mawaka sanye da kakin soji suna wasa a birnin Khartoum.

A arewacin Sudan, sojojin sama na gudanar da aikin soji na hadaka da kasar Masar.

"A bayyane take cewa suna kokarin nuna daga sanda ne wa kasar Ethiopia," a cewar Birgediya Mahmoud Galender mai murabus a hirarsa da BBC.

A nata bangaren, Ethiopia ta ci gaba da kokarin bayar da tabbaci ga Sudan cewa madatsar ruwan ta Gerd ba za ta lalata kasar ba.

A ranar Lahadi, Firaiminista Abiy Ahmed ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa "ba shi da aniyar haifar da barazana" ga yankin kwarin kasar, ya kara da cewa cikar da ya yi a bara ko shakka babu ya kare kasar Sudan din daga mummunar ambaliyar ruwa."

Ya kuma yi magana a kan musayar bayanai game da abubuwan da ke faruwa gabanin damuna ta wannan shekarar.