Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 03Article 450568

BBC Hausa of Monday, 3 May 2021

Source: BBC

Gareth Bale ya ci wa Tottenham kwallo uku rigas

Gareth Bale Gareth Bale

Tottenham ta yi nasarar doke Sheffield United da ci 4-0 a wasan mako na 34 a gasar Premier League da suka fafata ranar Lahadi.

Hakan ya kara kwarin gwiwa ga kungiyar kan fatan da take yi na son buga gasar Zakarun Turai ta badi.

Tun kan hutu Gareth Bale ya fara cin kwallo, bayan da suka yi hutu suka koma karawa ta biyu ne ya kara biyu a ragar Sheffield United.

Tottenham ta kara na hudu ta hannun Heung-min Son, saura minti 13 su tashi daga fafatawar.

Dan kasar Koriya ta Kudu ya ci wata kwallo minti biyar da komawa zagaye na biyu, amma alkalin wasa ya kashe ta cewar ya yi satar gida.

  • Gareth Bale ya hana Madrid jin kunya
  • Gareth Bale ya roki Real Madrid, Shanghai Shenhua na nemansa
Da wannan sakamakon Tottenham tana mataki na biyar da tazarar maki biyar tsakaninta da ta hudu Chelsea, kuma saura wasa hurhudu a karkare kakar bana.

Sheffield United wadda ta fadi daga buga gasar Premier ta badi tun 17 ga watan Afirilu, bayan da Wolves ta doke ta, ta kai hari daya tal a ragar Tottenham.

Kuma golan Tottenham, Hugo Lloris bai fuskanci wani kalubale ba a kaco kan din fafatawar.

Wannan ne karo na biyu da Bale ya ci kwallo uku rigis a tarihin Premier League, bayan da ya fara a kan Aston Villa tun cikin watan Disambar 2012.