Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 27Article 450994

BBC Hausa of Thursday, 27 May 2021

Source: BBC

Garba Shehu na shan suka kan kare Buhari bisa kin halartar jana'izar sojoji

Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya

Ƴan Najeriya sun sake sako Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gaba, game da tsokacin da ya yi kan dalilin da ya sa shugaban kasar bai halarci jana'izar babban hafsan sojin ƙasar ba da sojoji 10 da suka mutu a hatsarin jirgin sama.

Rashin halartar Buhari wurin jana'izar sojojin ya ja hankalin ƴan Najeriya inda suka dinga sukar matakin shugaban da mataimakinsa na ƙauracewa jana'izar.

Tsokacin da Malam Garba Shehu ya yi game da batun a wata hirarsa da gidan talbijin na Arise TV a ranar Talata ya sake tsokano ƴan Najeriya inda suka dinga caccakarsa.

Garba Shehu, maitaimakawa Buhari kan harkokin watsa labarai, ya ce yana nahirar Turai lokacin da al'amarin ya faru kuma bai samu zantawa da shugaban ba amma ya bayar da misali cewa, Buhari mutum ne da ba ya son ana rufe hanyoyi ana cin mutunci da zarafin mutane da nufin samar da tsaro da hanyar a zai wuce.

"Shin ko kun san dalilin da ya sa yanzu [Shugaba Buhari] yake Sallar Juma'arsa a fadar shugaban ƙasa ba ya zuwa babban Masallacin kasa? Saboda ba ya son wannan ra'ayin na rufe hanyoyi, inda jami'an tsaro ke gallazawa mutane a kan hanya don shugaban kasa ya samu hanya."

Sai dai kalaman ba su gamsar da ƴan Najeriya ba, inda tun fitar da hirar a kafofin sadarwa na intanet suka dinga bayyana ra'ayoyi na sukar Garba Shehu kan dalilin da ya bayar na kare shugaba Buhari kan rashin halartar jana'izar sojojin.

Sunan Garba Shehu ya kasance ɗaya daga cikin batutuwan da aka fi tattaunawa a Najeriya a ranar Laraba inda galibin ƴan Najeriyar masu tsokaci suke ganin don kada a rufe hanya ba zai zama dalili ƙin halartar Buhari wurin jana'izar ba.

Wasu sun ta jefa tambayoyi da suke buƙatar Garba Shehu ya amsa masu.

@BhadmusAkeem ya ce: Janar ɗin soja huɗu, Laftanal Janar ɗaya da Birgediya Janar uku su mutu a hatsarin jirgin sama yayin da suke yi wa ƙasa aiki, amma Garba Shehu ya yi tunanin rufe hanya ga shugaban don zai halarci jana'iza wani babban abu ne da ba za a iya sadaukarwa gare su ba.



@Horlamilekan_Ay ya ce: Mai magana da yawun shugaban ƙasa Garba Shehu ya ce Buhari bai halarci jana'izar Babban hafsan soji ba saboda cunkoson ababen hawa. Amma lokacin yaƙin neman zaɓen 2019 ba cunkoso kenan? Ba a ci zarafin mutane ba lokacin.


@jeffphilips1 ya ce: Me ya faru da hilikwaftan da yake hawa zuwa Daura? Ba fa wanda zai kashe Garba Shehu idan har bai amsa ko wace tambaya ba a matsayinsa na mai magana da yawun shugaba.



@AhmedGashinge ya ce: Don Allah Garba Shehu kada ka ƙara fusata mu. Mene ne nisan da ke tsakanin Mallacin Juma'a na ƙasa da fadar shugaban ƙasa inda aka yi Sallar jana'iza. Ko zuwa maƙabartar sojoji ba zai haifar da wani cikas ba ga hanyoyi domin mun san hanyoyin Abuja duka a buɗe suke.

@ByHimILive ya ce: Ya fi amfani Garba Shehu ya yi shiru.

A ranar Asabar a Abuja aka binne Babban Hafsan sojin Najariya Janar Attahiru tare da sojoji 10 da suka mutu a hatsarin jirgin sama a ranar Juma'a yayin wata ziyarar aiki daga Abuja zuwa Kaduna.

Sojojin da suka mutu sun ƙunshi Janar guda uku da suka haɗa da Birgediya Janar Kuliya babban jami'in leƙen asiri na sojin Najeriya da Birgediya Janar M Abdulkadir da kuma Birgediya Janar Olayinka.

Ministan tsaro ne ya wakilci Buhari a wurin jana'izar sojojin.

Da BBC ya tuntubi Malam Garba Shehu kan dalilin da ya bayar ya ce misali ya bayar amma wasu suka ɗauka matsayin shi ne dalilin da ya shugaba Buhari bai halarci jana'izar ba.

"Na bayar da misali ne da dalilin da ya sa yake Sallar Juma'arsa a masallacin fadarsa saboda ƴan sanda na takura wa mutane ana rufe titi, na ce watakila dalili kenan," in ji shi.