Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 02Article 449443

BBC Hausa of Tuesday, 2 March 2021

Source: BBC

GGSS Jangebe: Me ya sa ake satar ɗalibai a Najeriya?

ee ee

Tun watan Disamba, sama da ɗalibai 600 aka sace daga makarantu a arewa maso yammacin Najeriya, wanda ke nuna wani mummunan ci gaba mai matukar tayar da hankali a matsalar satar mutane domin neman kuɗin fansa.

Sace ɗaliban makarantar sakandare mata su 317 a garin Jangebe a jihar Zamfara shi ne karo na biyu cikin kwana 10 da ƴan bindiga suka abka makarantar sakandare suka saci ɗalibai bayan garkuwa da ƴan makarantar Kagara a jihar Neja a ranar 17 ga Fabrairu kafin a sake su a ranar Asabar.

Hukumomi sun ce masu fashin daji ne suka kai hare-haren a makarantun na arewa maso yammaci.

Ƴan ƙasar da dama sun yi imanin cewa akwai raunin a ɓangaren tsaro da gwamnoni waɗanda ba su da iko a kan tsaro a jihohinsu.

Ƴan sanda da sojoji duka suna ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya - kuma biyan kuɗin fansa, ya ƙara haifar satar mutane a matsayin wata babbar hanyar samun kuɗi.

Wannan zargi ne da gwamnonin suka musanta. Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, wanda a baya ya ba wa ƴan fashi" tubabbu" gidaje da kudi da motoci, ya ce mutane" ba su gamsu da shirin nasa na zaman lafiya ba "suna yin zagon kasa ga kokarinsa na kawo karshen rikicin.

Kafin yanzu, waɗanda aka fi yin garkuwa da su matafiya ne a yankin arewa maso yammacin Najeriya, waɗanda suka biya tsakanin dala 20 zuwa dala 200,000 domin tsira, amma tun sace ɗaliban makarantar Chibok 276 a 2014 da Boko Haram ta yi a jihar Borno, ƴan bindiga da dama sun bi tafarkin.

Kyautar mota da kuɗi ga ƴan bindiga

Sace ɗalibai a dama maimakon matafiya, ya fi jan hankalin duniya da kuma hukumomi domin ceto da ɗaliban wanda ke nufin biyan miliyoyin kuɗi a matsayin kuɗin fansa.

Mai sharhi kan sha'anin tsaro Kemi Okenyodo ya ce wannan wata babbar hanyar samun kuɗi ce ga ƴan bindiga.

"Ya kamata a sake duba batun biyan kudin fansa. Waɗanne hanyoyi ne ya kamata a diba da suka dace a bi wajen hana satar mutane don guje biyan fansar?" kamar yadda ya diga ayar tambaya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna cewa gwamnoni na ƙara rura wutar rikicin.

"Ya kamata gwamnni su sake nazari kan tsarin kyautatawa ƴan fashi da kuɗi da motoci. Irin wannan ba zai haifar da ɗa mai ido ba domin zai haifar da mummnan sakamako," in ji Shugaban.

State Governments must review their policy of rewarding bandits with money and vehicles. Such a policy has the potential to backfire with disastrous consequences. States and Local Governments must also play their part by being proactive in improving security in & around schools.

— Muhammadu Buhari (@MBuhari) February 26, 2021

Wanda ya jagoranci sace ɗaliban Kankara a jihar Katsina a watan Disamba ba a daɗe ba ya ce ya tuba inda ya miƙa makamansa ga gwamnatin Zamfara.

Auwalu Daudawa da sauran abokan fashinsa gwamna Matawalle ya yi masu alƙawalin gida, da kuma tallafi da za su inganta rayuwarsu.

A atan Yulin shekarar da ta gabata gwamnan Matawalle ya yi alƙawalin bayar kyautar shanu biyu ga duk biniga ƙirar AK-47 da ƴan bindiga suka miƙa.

Saɓanin wanda ya gada wanda ya fuskanci kakkausar suka kan yadda ya tafiyar da lamarin ƴan matan Chibok da aka sace, Shugaba Buhari bai fuskanci wannan adawar ba gme da satar 'yan matan, musamman saboda nsarar da aka samu daga tattaunawar da ta kai ga sakin wasu daga cikin 'yan matan na Chibok a farkon mulkinsa.

Magoya bayansa sun ce gwamnatinsa ta fi mayar da hankali wajen sako ɗaliban da aka sace, amma da dama daga cikinsu, da suka hada da Leah Sharibu, da Boko Haram ta sace a Dapchi a 2018, har yanzu ba a sake su ba.

Amma matsalar tsaro ta ƙara taɓarɓarewa a mulin Buhari - sau huɗu ana satar ɗalibai a mulkinsa.

Kuma uku daga ciki a yankinsa na arewa maso yammaci, wanda ya ƙara nuna girman taɓarɓarewar tsaro a yankin duk da hankalin duniya ya fi karkata ga rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashi.

Ko da yake jami'an tsaro na yaƙi da ƴan fashi a yankin, inda suka tarwatsa ƙauyuka a da ke dazukan yankin da ƴan bindigar suka mamaye.

Me aka yi don tabbatar da tsaron makarantu

Akwai shiri da aka ƙaddamar na tabbatar da tsaron makarantu bayan sace ɗaliban Chibok ta wanda ake kira "Safe School Initiative"

Shirin ya shafi kewaye makarantun domin tabbatar da tsaron ɗalibai daga barazanar Boko Haram a arewa maso gabashi.

Akalla dala miliyan 20 aka yi alƙawalin za a ware wa shirin na shekaru uku wanda ya samu goyon bayan jekada na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan ilimi Gordon Brown, tsohon Firaministan Birtaniya.

An gina wasu makarantu na wuccin gadi ƙarƙashin shirin amma babu tabbaci ko an kewaye makarantun yankin.

Ko da yake sace-sacen ɗalibai na baya bayan nan sun faru ne a yankin arewa maso yammaci, wanda shirin bai shafa ba, satar ɗalibai 110 a makarantar Dapchi a jihar Yobe ya diga ayar tambaya kan nasarar shirin.

Jami'an tsaro sun kafa shingayen bincike kusa da makarantun, amma hakan na nufin akwai makarantu da dama a yankin arewa da babu jami'an tsaro.

Wasu makarantun sun ɗauki ƴan banga aiki amma wannan ya zama ba shi da tasiri a kan' yan ta'addan da ke dauke da muggan makamai.

Wasu labaran da za ku so ku karanta:

    Satar mutane a Najeriya: Yaya munin lamarin yake? Kasashen duniya sun cika da mamakin yadda aka sace dalibai 317 Zamfara : Yadda masu garkuwa da mutane suka sace alkalai biyu