Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 26Article 450444

BBC Hausa of Monday, 26 April 2021

Source: BBC

Eric Bailly: Zai ci gaba da wasa a Old Trafford zuwa karshen kakar 2024

Eric Bailly, Mai tsaron bayan Manchester da tawagar Ivory Coast Eric Bailly, Mai tsaron bayan Manchester da tawagar Ivory Coast

Mai tsaron bayan Manchester Eric Bailly ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa karshen kakar 2024.United,

Mai shekara 27 dan kwallon tawagar Ivory Coast ya yi wa kungiyar wasa 100 tun komawarsa Old Trafford daga Villareal a 2016 kan fam miliyan 30.

Sai dai dan wasan ya kan yi fama da jinya a lokacin da yake buga wasanninsa a Ingila.

''Ina cikin farin ciki. Ban dauki lokaci ba wajen yanke hukuncin rattaba hannu kan kwantiragi ba - Ina kaunar kungiyar nan, ina kuma jin dadi buga tamaula a United. '' kamar yadda ya fada.

''Yanzu da zarar na ji sauki zan koma kan ganiyata, shi ne abin da ke gabana. Sabuwar kwantiragi kamar sabon kalubale zan fuskanta kuma a shirye nake.

Sabuwar yarjejeniyar da Bailly ya saka hannu wadda za ta kare a karshen kakar 2024 ta hada da za a iya tsawaita ta kaka daya idan ya ci gaba da taka rawar gani.