Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 26Article 450965

BBC Hausa of Wednesday, 26 May 2021

Source: BBC

El Rufa'i ya ciyo bashin da har jikoki ba za su iya biya ba – Jam'iyyar PDP

Nasir El-rufa'i, Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufa'i, Gwamnan jihar Kaduna

Babbar jam`iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta zargi gwamnatin jihar Kaduna karkashin Mallam Nasiru El-Rufai da wasa da makomar al`ummar jihar ta hanyar cin bashin da zai iya zama alakakai ga al`ummomi masu tasowa.

Jam`iyyar PDPn ta ce a cikin shekaru shidan da suka wuce, gwamnatin APC mai mulkin jihar ta ci bashin da ya kai naira biliyon dari da saba`in, kuma babu wani abin nunawa na wannan kudin.

PDp dai ta yi zargin cewa babu ranar biyan bashin amma tuni jam`iyyar APC ta musanta zargin.

A cewar Manjo Yahaya Ibrahim Shunku mai ritaya, jigo a PDP ya bayyana wa BBC cewa gwamnatin El Rufa'i kadai ya karbi bashin dala miliyan dari uku da arba'in da daya a shekarar 2020.

"Lokacin da wannan gwamnati ta APC ta zo a shekara ta 2015, ana bin jihar Kaduna bashin sama da dala miliyan dari biyu da ashirin da shida - kusan gwamnoni 15 kafin zuwan wannan gwamnati." in ji Shunku.

PDP dai ta nemi gwamnatin ta Kaduna ta fito ta yi wa jama'a bayani kan abin da yake faruwa kafin lokaci ya kure.

Sai dai APC a martaninta ta ce abin da PDP take ba abin mamaki bane kuma adawa ce kawai.

Sakataren APC a Kaduna, Yahaya Baba Pate ya ce "abokin hamayya ai kullum ba zai yi maka adalci ba' saboda mutanen jihar sun san cewa gwamnati ta ciyo bashin domin ci gaban al'umma.

Ya ce al'ummar jihar Kaduna suna ganin amfanin bashin wajen gyare-gyaren tituna da asibitoci da kuma makarantu.

A cewarsa, akwai banbanci tsakanin bashin da El Rufa'i ya ciyo da na sauran gwamnonin da suka gabata saboda "bashi ne da akwai saukin biya, bashi ne da ba ruwa a ciki".

A don haka ya ce batun da PDP take yi "ba magana ba ce da mai hankali zai ɗauka, a gwamnatinmu muna da masana da suke ba gwamnati shawara kan ko mene gwamnati za ta shiga".

Batun ciyo bashi da gwamnatoci ke yi dai abu ne da ake tafka muhawara a kai inda masana tattalin arziki ke ganin ba laifi bane ciyo ba shi wajen bunkasa tattalin arziki sai dai jam'iyyun hamayya na zargin cewa sau da yawa bashin na karewa ne a aljihun masu mulki da majibantansu.