Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 11Article 449599

BBC Hausa of Thursday, 11 March 2021

Source: BBC

An sauya wajen da Man City za ta kara da Gladbach

'Yan kwallon Man City 'Yan kwallon Man City

Hukumar kwallon kafa ta Turai, ta sauya wajen da Manchester City za ta karbi bakuncin Borussia Monchengladbach zuwa Budapest a Champions League.

Tun farko an tsara Gladbach za ta ziyarci Ingila domin buga wasa na biyu a gasar zakarun Turai, amma aka dage saboda dokar hana yada cutar korana.

Sai dai ba a sauya ranar buga wasan ba wato 16 ga watan Maris da lokacin da za su barje gumi kamar yadda aka tsayar tun da fari.

Birnin Budapest shi ne ya karbi bakuncin wasan farko da suka buga cikin watan Fabrairu a matsayin Gladbach mai masaikin baki.

Sun yi karawar a Budapest sakamakon dokar hana shiga Jamus da ta kafa ga kasashen da annobar ta yi wa kamari har da Burtaniya.

City ce ta yi nasara da ci 2-0 a karawar da suka yi a Puskas Arena, inda Bernardo Silva da kuma Gabriel Jesus suka ci mata kwallayen.

Watakila Man City ta kara da Juventus

Hotunan atisayen Man Utd da Man City

City wadda ke fatan lashe kofi hudu a bana ta ci gaba da zama ta daya a Premier League da tazarar maki 14, bayan da ta doke Southampton da ci 5-2 ranar Laraba.

City ta kai wasan karshe a Caraboa Cup, sannan tana buga FA Cup na bana.