Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 29Article 451023

BBC Hausa of Saturday, 29 May 2021

Source: BBC

David Alaba: Real Madrid ta dauki dan wasan Bayern Munich

David Alaba ya koma Real Madrid daga Bayern Munich David Alaba ya koma Real Madrid daga Bayern Munich

Kungiyar kwallon kafar Real Madrid ta cimma yarjejeniya da David Alaba domin ya murza mata leda tsawon kakar wasanni biyar.

Kungiyar bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafinta na intanet ranar Juma'a.

A cewarta za a kaddamar da David Alaba a matayin sabon dan wasan Real Madrid bayan kammala 2021 European Championship.

Dan wasan dan kasar Austria da ke tsaron baya ya je Bayern Munich ne a 2008.

Alaba, mai shekara 28, ya taimaka wa Bayern wajen daukar kofin Champions League a 2013 da 2020.