Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 04Article 449471

BBC Hausa of Thursday, 4 March 2021

Source: BBC

Coronavirus a Najeriya: Mutum 464 sun kamu ranar Laraba

Mutum 464 sun kamu ranar Laraba Mutum 464 sun kamu ranar Laraba

Wannan shafi ne da yake kawo muku bayanan adadin masu kamuwa da cutar korona kullum a Najeriya, daga bayanan hukumar NCDC. Muna sabunta shi ne da zarar an samu sabbin bayanai kullum.

Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 464 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Laraba.

Bisa sabbin alkaluman hukumar, a wannan rana, jihar Legas ce ke kan gaba a jerin jihohin da aka samu ɓullar cutar da mutum 131 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 69 a jihar Kaduna da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

Mutum 33 kuma sun kamu da korona a Akwa Ibom sai Imo mai mutum 31, da jihar Katsina da aka gano mutane 30 da gwajin da aka yi musu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar.

A Kano an gano mutane 26 da suka kamu da cutar korona ranar ta Laraba.

Ga yawan wadanda aka samu a wasu jihohi

    Ondo-23 Yobe-20 FCT-18 Ogun-13 Rivers-12 Kebbi-11 Ekiti-9 Osun-6 Oyo-6 Borno-5 Gombe-5 Plateau-5 Edo-4 Abia-3 Delta-3 Zamfara-1
NCDC ta ƙara da cewa a ranar ta Laraba, mutum 16 sun mutu sannan an sallami mutum 1,280 daga cibiyoyi daban-daban da ke faɗin Najeriya.

Ya zuwa yanzu, alƙaluman masu cutar ta korona a ƙasar sun kai 156,963, an sallami 135,831 jumulla, sannan mutum 1,939 sun mutu tun bayan da cutar ta ɓulla a Najeriya.

    Coronavirus: Taswirar da ke nuna yawan wadanda suka kamu a duniya Adadin masu coronavirus a kasashen Afrika Coronavirus: Abubuwan da ya kamata ku dinga yi

Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar coronavirus

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.

Yaya zan kare kaina daga cutar?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

    Coronavirus: Wanne rukunin mutane ne ya fi hatsarin kamuwa da cutar? Yadda ake warkewa daga cutar coronavirus Coronavirus: Shin annoba ba ta shiga garuruwan Makkah da Madina? Tarihin manyan annoba da suka shafi arewacin Najeriya